Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Zimbabwe ya yi kira da a hada hannu don yaki da taaddanci a SADC
2020-05-20 11:43:15        cri

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, kana shugaban sashen siyasa da tsaro na kungiyar raya kasashen kudancin Afirka (SACD), ya yi kira ga kasashe mambobin kungiyar, da su hada kai don ganin bayan barazanar ta'addanci dake karuwa a shiyyar.

Shugaban ya bayyana haka ne yayin bude taron shugabanni uku na kungiyar, don tattauna yadda al'amuran tsaro suka tabarbare a wasu sassan Mozambique sakamakon ayyukan kungiyoyin 'yan ta'adda na Islama.

Mnangagwa ya bayyana cewa, kamar yadda lamarin yake a baya, wajibi ne kasashen na SADC su hada kai don ganin bayan wannan matsala dake karuwa wadda ka iya kawo cikas ga zaman lafiya, da ma ci gaban shiyyar.

A don haka, ya ce ya zama tilas, su hada hannu don tunkarar wannan matsala da ma sauran kalubale da shiyyar ka iya fuskanta yayin da suke aiki tare. Kuma za su yi galaba.

Taron kolin na yini guda da ya gudana a Harare, babban birnin kasar Zimbabwe don duba bukatar taimako da kasar Mozambique ta gabatar kan yadda za a yaki masu tayar da kayar baya, ya samu halartar shugabannin kasashen Bostwana da Zambia, da kuma Mozambique.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China