Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babbar kantomar Hong Kong ta yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su girmama hakkin Sin na tabbatar da tsaron kasa
2020-06-30 21:49:51        cri
A yau Talata ne aka kaddamar da taro karo na 44, na kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD, a birnin Geneva na kasar Switzerland, inda babbar kantomar yankin Hong Kong na kasar Sin Madam Carrie Lam Cheng Yuet-ngor, ta yi jawabi ta kafar bidiyo.

Cikin jawabin nata, jami'ar ta yi kira ga gamayyar kasa da kasa, da su girmama hakkin kasar Sin na kafa doka don tabbatar da tsaron kasa. A cewarta, batun tsaro ya shafi daukacin al'ummar kasar Sin, don haka bai kamata a kaucewa kafa wata dokar da ta shafi tsaron kasa a Hong Kong ba. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China