Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sanarwar kasashen yamma guda hudu ba za ta girgiza niyyar kiyaye yankin Hong Kong na kasar Sin ba
2020-05-29 21:11:42        cri
A ranar 22 ga wata, wato ranar da aka bude zama na 3 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin (NPC) karo na 13, kasashen uku da suka hada da Burtaniya, Canada da Australia sun bayar da sanarwa game da yankin musamman na Hong Kong, sanarwar da ta kasance tsoma baki ce cikin harkokin gidan kasar ta Sin. Daga baya kuma, a gabannin rufe babban taron, kasashen yamma guda hudu, wato Burtaniya, Amurka, Canada, Autralia, sun bayar da sanarwa game da Hong Kong, ba tare da yin la'akari da ra'ayin mazauna yankin ba.

A gun taron na NPC, wakilai 36 da suka fito daga yankin Hong Kong, tare da wakilai na sauran jihohi da larduna, sun jefa kuri'u kan daftarin kafa dokokin kiyaye tsaron kasa na Hong Kong. A yammacin ranar 28 ga wata kuma, an zartas da kuduri game da hakan, bisa yawan kuri'un goyon baya da aka samu.

Bayan fitar da babbar dokar yankin Hong Kong da aka wallafa da Sinanci, da Turanci, wadda ake iya dubawa da karantawa a shafin yanar gizo ta gwamnatin yankin Hong Kong, marubucin sashi na musamman na kasar Burtaniya Tom Fowdy, a kwanakin baya ya sanya wata ayar dake cikin babbar dokar a saman shafin dandalin sada zumuncinsa, inda ya rubuta cewa, "Aya ta 18, sashi na 2 na babbar dokar ta Hong Kong ta jaddada cewa, idan an samu yanayi na halin gaggawa a yankin, ta yadda hakan zai kawo barazana ga dinkuwar kasa ko tsaron kasa, kuma gwamnatin yankin ba ta iya shawo kan hakan ba, to majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na da ikon kafa dokoki game da yankin Hong Kong."

Kafofin watsa labaru na kasashen yamma suna ganin cewa, majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta kaddamar da wannan kudurin ne a cikin wani lokacin da ya dace, kasashen yamma dake tinkarar annobar COVID-19 ba su iya mayar da martani cikin lokaci ba, suna mamaki sosai. Kalmominsu na tsoratar da kasar Sin ma, ba su da wani tasiri na fargitarwa, kuma ba su da wani tushe.

Game da tsoma baki da 'yan siyasar Burtaniya suka yi, jakadan kasar Sin dake kasar Liu Xiaoming, ya wallafa a shafin dandalin sada zumunci cewa, "Wani yankin Hong Kong mai zaman karko da wadata, na dacewa da moriyar kasashen Sin da Burtaniya, kuma kamata ya yi kasar Burtaniya ta girmama babbar moriyar kasar Sin, ta dakatar da tsoma baki cikin harkokin Hong Kong, ta kuma dauki matakai masu amfani wajen wadatar da yankin. (Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China