Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'an NRM: Tsarin Sin ta mayar da jama'a a gaban komai shi ne nasarar ci gaban kasar da ma yaki da COVID-19
2020-06-25 15:29:38        cri

Mataimakin sakataren jam'iyyar NRM mai mulkin kasar Uganda Richard Todwong da shugaban matasa na jam'iyyar Augustine Otuko, sun bayyana cewa, duniya na bukatar koyi da akidar kasar Sin ta mayar da jama' a a gaban komai, tsarin da a cewarsu, shi ne kashin bayan ci gaban tattalin arziki da rayuwar al'ummar Sinawa da ma nasarar da kasar ta samu a yaki da COVID-19.

Jami'an sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin cewa, fahimtar da wannan tsari ne, ya sa JKS ta ke jagorantar kasar bisa turbar raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma.

Otuka ya ce, a karkashin tsarin JKS akwai tsari na tuntuba game da bukatun da suka shafi al'ummar Sinawa. Manufar haka ita ce, yin gyara ko ci gaba a wuraren da suka dace. Hakan ya sanya jama'a zama kashin bayan jam'iyyar.

Ya ce, ya kamata shugabanni a fadin duniya, su rungumi tsarin mayar da jama'a a gaban komai yayin da suke tsara manufofi, yin haka na sanya jama'a da hukumomin ba da tasu gudummawar wajen aiwatar da duk wata ajandar raya kasa.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China