Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin saman Najeriya sun kashe wasu mayakan BH a shiyyar arewa maso gabashin kasar
2020-06-21 16:12:23        cri

Rundunar sojojin Najeriya ta ce jerin hare haren da dakarun sojojin saman Najeriyar suka kaddamar sun yi sanadiyyar kashe mayakan Boko Haram masu yawa a dajin Sambisa dake shiyyar arewa maso gabashin kasar.

John Enenche, kakakin rundunar sojojin Najeriyar ya fada cikin wata sanarwa cewa, sojojin sun kaddamar da hare haren ne a ranar Juma'a a yankin Bula Korege, yankin da ya kasance a matsayin cibiyar jigilar da kayayyaki da maboyar kungiyar 'yan ta'addan dake bakin dajin Sambisa.

Enenche ya ce, a hare haren na ranar Juma'ar, sojojin sun yi nasarar lalata wata motar daukar bindigogi ta 'yan ta'addan.

Ya ce jiragen saman yakin dakarun sojojin Najeriyar sun lalata wasu gine-ginen dake maboyar mayakan da kuma hallaka wasu 'yan ta'addan. Sai dai jami'in sojojin bai bayyana adadin mayakan Boko Haram da aka kashe ba a lokacin hare haren da sojojin suka kaddamar a yankin.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China