Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: kasashen Afrika ne za su fara amfana da allurar rigakafin cutar COVID-19 da kasar Sin take fatan samarwa
2020-06-17 23:53:16        cri
A yayin taron kolin Sin da Afirka na musamman kan hadin gwiwar yaki da COVID-19 da aka shirya a yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi alkawarin a cikin jawabinsa, cewa bayan kasar Sin ta kammala nazari da samar da allurar rigakafin cutar COVID-19, kasashen Afirka ne za su fara amfana.

Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga bangaren Afirka wajen yakar cutar, da kara samar wa kasashen Afirka tallafin kayayyaki da turo tawagogin kwararru a fannin aikin jinya zuwa kasashen Afirka, da taimakawa kasashen Afirka wajen sayen kayayyakin dakile cutar a nan kasar Sin. Kana, kasar Sin za ta soma gina hedkwatar shawo kan cututtuka ta Afirka a bana, wato kafin lokacin da aka tsara, da gaggauta gina asibitin sada zumunci tsakanin Sin da kasashen Afirka da karfafa hadin kai a tsakanin asibitocin kasashen biyu, da nufin gina al'umma mai kykkyawar makoma ta bai daya a fannin kiwon lafiyar bangarorin biyu. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China