Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: Sin za ta yafe wa kasashen Afirka da abin ya shafa basusukan da take binsu ba tare da ruwa ba
2020-06-17 23:54:33        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a gun taron kolin Sin da Afirka kan hadin gwiwar yaki da cutar Covid-19 da ya gudana yau Laraba cewa, kasar Sin za ta soke bashin da take bin wasu gwamnatocin kasashen Afirka da babu kudin ruwa a ciki wadanda ya kamata su biya a karshen shekarar 2020. Ga kasashen na Afirka da COVID-19 ta yiwa mummunar illa kana suke da matsalar kudi, kasar Sin za ta yi aiki da ragowar kasashen duniya wajen ba su taimakon da ya dace, har ma za a iya kara wa'adin dakatar da biyan bashin, don taimaka musu fita daga wannan matsala. Kasar Sin tana karfafawa hukumomin kudinta gwiwar su goyi bayan shirin dakatar da biyan bashi na G20 (DSSI) su kuma shirya tattaunawa da kasashen Afirka bisa manufofin kasuwa. Ya kuma yi kira ga G20, da ta taimaka wajen dakatar da biyan bashin ga kasashen da wannan batu ya shafa, ciki har da wadanda ke Afirka.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China