Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Sudan za ta daddale yarjejeniya da kungiyoyi masu dauke da makamai
2020-06-11 09:45:47        cri

Mataimakin shugaban majalisar mulkin kasar Sudan ya sanar a ranar Laraba cewa, ana sa ran za'a rattaba hannu kan cikakkiyar yarjejeniyar zaman lafiyar kasar tsakanin gwamnati da kungiyoyi masu dauke da makamai nan da ranar 20 ga watan Yuni.

Mohamed Hamdan Daqlu, ya bayyana a taron cimma matsaya ta kafar bidiyo tsakanin bangaren gwamnati da kungiyoyi masu dauke da makamai cewa, gwamnatin kasar tana samun ci gaba wajen cimma nasarorin yarjejeniyar zaman lafiyar kasar, kana ya ce sun yiwa al'ummar kasar Sudan alkawarin za'a sanya hannu kan cikakkiyar yarjejeniyar zaman lafiyar mai dorewa nan da ranar 20 ga watan Yuni.

Ya ce ana shirin kammala dukkan shirye shiryen da suka dace domin cimma matsaya ta karshe wadda ta shafi batun raba madafun iko gabanin rattaba hannu kan yarjejeniyar.

Tun a watan Oktoban bara, babban birnin Sudan ta kudu Juba yake karbar bakuncin tarukan tattaunawar zaman lafiyar tsakanin gwamnatin kasar Sudan da kungiyoyin 'yan tawayen daga yankunan Darfur, da kudancin Kordofan da shiyyoyin jihar Blue Nile.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China