Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dakarun gwamnatin Sudan sun sake kwace ikon ginin hukumar tsaron kasar
2020-01-15 13:00:31        cri

Shugaban majalisar mulkin kasar Sudan Abdel Fattah al-Burhan ya ce a ranar Laraba dakarun gwamnatin kasar sun sake kwace ikon ginin babbar hukumar tattara bayanan sirri ta kasar (GIS), wanda dakarun 'yan tawaye suka kwace ikon ginin a ranar Talata.

Al-Burhan ya fada a taron manema labarai ranar Laraba cewa, dukkan helkwatocin hukumomin ayyukan tsaron kasar ta GIS suna karkashin ikon dakarun sojojin gwamnatin kasar a yanzu.

Al-Burhan ya ba da sanarwar ci gaba da ayyukan sararin samaniyar kasar a filin jirgin saman kasa da kasa dake Khartoum, wanda huhumomin kasar suka rufe na tsawon sa'o'i biyar a matsayin riga kafi.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China