Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sama da mutane 20 sun mutu ko sun bace sanadiyyar ambaliyar ruwa a kudancin kasar Sin
2020-06-11 15:17:43        cri

Sama da mutane 20 sun mutu ko kuma sun bace bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka sheka wanda ya yi sanadiyyar ambaliyar ruwa da zaftarewar laka a kudancin kasar Sin, bisa ga rahoton da jami'an yankin suka fitar.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar Sin ta ce, ya zuwa karfe 2 na yammacin ranar Talata, an samu mamakon ruwan sama wanda ya haifar da ambaliyar ruwa kuma ya shafi mutane kusan miliyan 2.63 daga larduna 11.

A cewar ma'aikatar, ruwan saman da aka sheka ya sa an sauya matsugunai ga mutane kimanin 228,000, sannan gidaje sama da 1,300 sun lalace, lamarin da ya haddasa hasarar tattalin arziki na sama da yuan biliyan 4 kwatankwacin dala miliyan 566.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China