Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An fara amfani da jirgin ruwa mai alkahura dake sahun gaba a duniya mai suna "Hai Long"
2019-12-31 11:01:46        cri

Jiya Litinin, an fara amfani da jirgin ruwa mai ba da taimako ga aikin yin alkahura mai suna "Hai Long" a birnin Guangzhou, jirgin ya kasance irinsa mafi karfi a kasar Sin. "Hai Long" zai iya ba da taimako ga masu aikin alkahura ta hanyar isa yankin ruwa mai zurfi da zurfinsa zai kai fiye da daruruwan mitoci, ana kuma iya amfani da shi wajen habaka albarkatun teku da aikin ceto a teku da aikin nazarin kimiya da binciken albarkatun ma'adinai da dai saransu cikin lokaci mai tsawo. Hakan ya sa, "Hai Long" na da kwarewa da saukaka da ba da tabbaci da tsaro, matakan da ya sa ya kasance a sahun gaba a duniya a wannan fanni. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China