Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya jaddada wajibcin gina ingantacciyar tashar cinikayya ta ruwa cikin 'yanci dake tsibirin Hainan
2020-06-01 16:28:08        cri
A kwanan nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi muhimmin bayani kan aikin gina tashar cinikayya ta ruwa cikin 'yanci dake tsibirin Hainan, inda a cewarsa, gina tashar, wani muhimmin kuduri ne da kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar ya yanke, wanda ya dace da halin da ake ciki a gida da waje, da zummar neman ci gaba bisa salon musamman irin na tsarin gurguzu.

Xi ya nanata cewa, dole ne a maida hankali sosai kan yin kirkire-kirkire ga tsare-tsaren tashar, da canja salon tunani, da kuma kokarin fitar da sabbin tsare-tsare ba tare da kasala ba. Ya ce ya zama dole a goyi-bayan gwamnatin Hainan don yin kirkire-kirkire, da samun sabon ci gaba wajen gina tashar cinikayya ta ruwa cikin 'yanci a wurin.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China