Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta sha alwashin gaggauta kammala tashar ruwa ta cinikayya maras shinge a Hainan
2020-04-14 11:06:42        cri

Jami'i a ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin Tang Wenhong, ya ce mahukuntan kasar sun sha alwashin gaggauta kammala tashar ruwa ta yankin cinikayya maras shinge a lardin Hainan dake kudancin kasar.

Jami'in ya ce aiki wani bangare ne na bunkasa manufar kara bude kofa ga kasashen waje ta tsibirin na Hainan. Ya ce tuni lardin Hainan ya cimma manyan nasarori, ya kuma fadada dukkanin ayyukan cimma nasarar wannan manufa, tun bayan kafuwar yankin gwaji na cinikayya maras shinge, karkashin tsarin da aka kaddamar a shekarar 2018.

Karin fannin da aka cimma nasara shi ne, bincike da ba da dama ga 'yan kasuwa, da bunkasa hada hadar cinikayya, da zuba jari, musamman wadanda ke da nasaba da gina tashar ruwa ta cinikayya maras shinge, baya ga nasarar aiwatar da sama da kaso 97 bisa dari na ayyukan gwaji da aka gabatar a shekarar 2018.

Sakamakon aiwatar da wadannan matakai, Hainan ya kara bude kofar sa ga sauran sassan duniya. Kaza lika lardin ya samu karin sabbin kamfanoni masu jarin waje, kana a shekarar 2019, jarin waje da aka zuba a lardin ya ninka da kaso sama 100 a shekara daya.

Tang ya kara da cewa, lardin Hainan zai fadada kirkire kirkire a fannin gudanarwa, zai kuma yada fasahohin sa ga sauran sassan kasar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China