Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Fim din Murnar cika shekaru 70 da kafuwar sabuwar kasar Sin ya samu lambar yabo ta musamman a bikin fina-finan kasa da kasa na Hainan
2019-12-09 09:59:41        cri

A jiya Lahadi, fim da babban gidan rediyo da telibijin na kasar Sin CMG mai suna "Murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyyar jama'ar kasar Sin", ya samu lambar yabo ta musamman, a bikin fina-finan kasa da kasa na Hainan karo na biyu.

Wannan fim ya daidaita ingancin hoton bikin kafuwar sabuwar kasar Sin, da kuma kyautata launin hoton da fasahar zamani ta 4K, da murya mai ma'aunin 5.1. An gudanar da wannan biki ne a Hainan, daga ran 1 zuwa 8 ga wata, inda masu kallo suka shakata da wannan fim mai faranta zuciya.

Bayan bikin kafuwar sabuwar kasar Sin, CMG ta gabatar da wannan fim da harshen Cantonese, da kuma harsunan kananan kabilu 5, da kuma fim mai suna "Faretin soja na shekarar 2019" da harsunan ketare 6, matakin da ya hada wannan biki da al'ummar duniya.

Ban da wannan kuma, wannan fim mai taken "Murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyyar jama'ar kasar Sin", an rika kyautata ingancinsa da kimiyya da fasahohin zamani, kuma an gabatar da shi a ran 15 ga watan Nuwamba, a gidajen sinima daban-daban na kasar Sin. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China