Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Guinea Bissau ta tsawaita dokar ta baci a kasar har zuwa ranar 10 ga watan Yuni
2020-05-27 09:47:07        cri

Shugaban kasar Guinea Bissau, Umaro Sissoco Embalo, ya yanke shawarar tsawaita dokar ta baci a kasar da karin kwanaki 15, har zuwa ranar 10 ga watan Yuni.

Cikin wata dokar shugaban kasa, shugaban ya ce ya dauki matakin ne bayan nazarin yanayin cutar COVID-19 a kasar, yana mai cewa yanayin bai sauya ba cikin kwanaki 15 da suka gabata, lokacin da kasar ta samu wadanda suka harbu da cutar da dama.

Ya ce abun damuwa ne, yadda ake samun karuwar masu kamuwa da cutar. Yana mai cewa a bayyane yake cewa, dole ne a ci gaba da daukar matakan kariya da shawo kan annobar.

Ya kara da cewa, za a ci gaba da aiwatar da dokar hana fita daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safiya, kuma har yanzu za a bari mutane su bar gidajensu ne tsakanin karfe 7 na safiya zuwa 2 na rana, domin cefene.

Shugaba Embalo ya yi kira ga al'ummar kasar su rika nisantar juna da sanya makarin hanci da baki a duk lokacin da suka fita, yana mai cewa, gwamnati za ta samar da sabbin matakan da za su shawo kan tasirin cutar kan kiwon lafiya da tattalin arziki. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China