Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Guinea Bissau mai ci ya amince da shan kaye a zabe
2019-11-29 13:11:54        cri

Jose Mario Vaz, shugaban kasar Guinea-Bissau mai ci, ya amince da faduwa a zaben, wanda aka gudanar a ranar Lahadi, kamar yadda ya bayyana a taron manema labarai ranar Alhamis a Bissau, ya tabbatar da cewa zai amince da sakamakon zaben.

Sai dai kuma, dan takarar mai zaman kansa wanda ya zo na hudu bayan kammala zagayen farko na zaben ya yi ikirarin cewa, an samu kura-kurai lokacin gudanar da zaben.

Vaz ya ce, akwai kura-kurai da aka samu a shiyyar gabashin kasar, wadanda suka hada da satar kuri'u da dangwala kuri'u tun gabannin ranar zabe.

Sai dai Vaz ya ce zai sadaukar da kansa wajen yin abin da ya dace kuma zai iya rungumar kaddara.

Za'a gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasar ta Guinea-Bissau a ranar 29 ga watan Disamba, kamar yadda sakamakon farko da hukumar zaben kasar NEC ta wallafa a ranar Laraba.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China