NPC: Za a kara sa ido kan manyan ayyuka game da ci gaban tattalin arziki da al'umma
Har yanzu ana ci gaba da gudanar da babban taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato NPC a nan birnin Beijing. Rahoton ayyuka da aka gabatar a yau ga zaunannen kwamitin majalisar don dubawa ya nuna cewa, a shekarar 2020, zaunannen kwamitin zai ci gaba da dora muhimmanci kan inganta da sa ido kan manyan ayyukan da suka shafi ci gaban tattalin arziki da al'ummar kasar, wadanda suka hada da binciken yadda ake aiwatar da wasu muhimman dokoki a fannonin kiyaye namun daji, da jin kai, da yin takara ba bisa doka ba da dai sauransu. Kana za a yi tambayar musamman kan yadda ake kandagarki da shawo kan matsalar gurbatar kasa, da yadda ake magance manyan matsalolin da aka binciko, da kuma yin bincike da nazari kan ayyukan yiwa tsarin inshorar al'umma kwaskwarima da dai sauransu.
Baya ga haka, rahoton ya kuma nuna cewa, a shekarar bana, zaunannen kwamitin majalisar zai kara karfin kafa dokoki a fannin kiwon lafiyar al'umma, da yin gyare-gyare kan dokokin kiyaye namun daji, da na kandagarki da shawo kan cututtuka masu yaduwa, da na binciken kiwon lafiya, da tinkarar lamuran ba zata, da na lafiyar halittu da dai sauransu. (Bilkisu)