Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kira taro karo na 17 na zaunannen kwamitin NPC na 13 a nan birnin Beijing
2020-04-26 20:44:28        cri

Yammacin yau Lahadi, an kira cikakken zaman taro karo na 17 na zaunannen kwamitin majalisar kafa dokoki ta kasar Sin, NPC na 13 a nan birnin Beijing, shugaban majalisar NPC Li Zhanshu ya jagoranci taron.

A watan Fabrairu na bana, zaunannen kwamitin ya gabatar da wani kuduri mai taken "Hana haramcin cinikayyar dabobbin daji da hana cin naman daji don tabbatar da lafiyar jikin jama'a", inda aka tanadi sharudan bada izini da kuma bincike kan amfani da sassan jikin dabobbin daji amma ban da cin namansu, kuma ana bukatar shigar da wadannan batutuwa cikin doka. Kwamiti mai kula da sha'anin noma da kauyuka na NPC ya gabatar da rahoto dangane da hakan, don a yiwa dokar kandagarki dangane da dabobbi gyaran fuska.

Ban da wannan kuma, taron ya tattauna kan wasu manyan abubuwan dake da alaka da zaman rayuwar jama'a da bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin.

Taron kuma ya zartas da daftarin dabarun kada kuri'u kan taro karo na 17 na zaunannen kwamiti na NPC na 13. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China