Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manyan kusoshin kasashen Afirka sun yi kira da a daidaita tsarin kula da duniya
2020-05-25 12:19:44        cri
Mamban majalissar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar, mista Wang Yi, ya gabatar da shawarwari guda 3 game da aikin kyautata tsarin kula da duniya, a wajen wani taron manema labaru da ya gudana a jiya Lahadi, a gefen tarukan majalissun kasar Sin da ke gudana a halin yanzu.

Bayan sauraron maganar mista Wang, wasu masana da manyan jami'ai na kasashen Afirka, sun nuna amincewa da manufar da kasar Sin ta gabatar, tare da nanata cewa, yunkurin adawa da dunkulewar duniya, da neman daukar matakan kariya na kashin kai, ba shi da amfani ko kadan.

Cikin wadannan manyan kusoshin, har da wani shehun malami mai nazarin batutuwa masu alaka da Afirka da Sin na kasar Najeriya, mista Adekunle, wanda ya ce ya yarda da kiran da kasar Sin ta yi, na kafa al'ummar dan Adam mai makoma ta bai daya ta fuskar kiwon lafiya, saboda wannan aiki ya shafi ingancin zaman rayuwar daukacin dan Adam. A cewarsa, yanzu haka dukkan mutanen duniya na kokarin yaki da annobar COVID-19, kana ba za a samu nasara a wannan yunkuri ba, har sai an yi watsi da bambancin kabila, da kiyayya, a kuma karfafa hadin gwiwa tsakaninsu, don neman ci gaban al'ummun duniya baki daya. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China