Masanin kasar Kenya ya ce kasar Sin ta yi daidai wajen magance saka wani mizani a fannin tattalin arziki
Stephen Ndegwa, shehun malami mai nazarin manufofin da suka shafi jama'a, gami da batun kasar Sin, na jami'ar USIUA (the United States International University-Africa) ta kasar Kenya, ya yi nazari kan rahoton gwamnatin kasar Sin na shekarar 2020 da firaministan kasar Li Keqiang ya gabatar, jiya Juma'a, a wajen taron wakilan jama'ar kasar dake gudana a birnin Beijing na kasar Sin. Shehun malamin ya ce yadda gwamnatin kasar Sin ta magance saka wani mizanin karuwar tattalin arzikinta a wannan shekarar da muke ciki, ya yi daidai, saboda annobar COVID-19 da ta ki ci ta kicinyewa na ta haifar da matsaloli ga tattalin arzikin duniya, lamarin da zai shafi dukkan kasashe.
Haka zalika, masanin ya ce yadda kasar Sin ta samu shawo kan yaduwar cutar COVID-19 a cikin gida, wani sakon albishir ne ga sauran kasashe. Domin wannan ci gaban da kasar Sin ta samu ya shaida cewa, za a iya farfado da tsari da oda gami da tattalin arzikin wata kasa, illa dai gwamnati ta saka buri mai dacewa, gami da jaroranci yadda ya kamata, musamman ma a fannin dakile yaduwar cutar COVID-19. (Bello Wang)