Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bangarori daban daban na Afirka sun yabawa aniyar Sin ta kara bude kofa ga ketare
2020-05-24 16:55:48        cri

 

Kiran manyan taruka biyu na kasar Sin na bana, ya jawo hankulan duk duniya, ciki har da bangarori daban daban na nahiyar Afirka. A cikin 'yan kwanakin nan, 'yan jaridar CMG sun yi hira da wasu jakadun kasashen Afirka dake nan kasar Sin, inda suka nuna yabo sosai kan aniyar kasar a fannonin kara bude kofa ga kasashen ketare, da bada tabbaci ga tsarin sana'o'i da na samar da kayayyaki, da kuma inganta yin kwaskwarima da bunkasuwa ta hanyar bude kofa.

 

 

Jakadan kasar Senegal dake kasar Sin Mamadou Ndiaye, ya dora muhimmanci sosai kan manufar kasar Sin ta inganta dunkulewar duniya da kasancewar bangarori da dama.

 

 

A nasa bangaren, jakadan kasar Algeria Ahcène Boukhelfa ya ce, kiran tarukan biyu da kasar Sin ta yi na da muhimmanci matuka, yana halartar tarukan a matsayin wakilin da ba zai jefa kuri'a ba a ko wace shekara. A cewarsa, ko shakka babu kasar Sin zata tsaida kuduri bayan nazarin yanayin bayan cutar COVID-19, matakin da zai kara karfin tattalin arzikin kasar, ta yadda za a iya kawar da tasirin da annobar ta haddasa. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China