Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hatsarin jirgin sama a Pakistan ya yi sanadin mutuwar mutane 97, yayin da mutum 2 suka tsira
2020-05-23 16:13:31        cri
Rundunar sojin Pakistan ta ce masu aikin ceto sun gano gawarwaki 97 daga baraguzan jirgin kasar na kamfanin Pakistan International Airlines, wanda ya fadi a wata unguwar jama'a a birnin Karachi dake kudancin kasar.

Wata sanarwa da sashen hulda da jama'a na rundunar sojin ya fitar, ta ce masu aikin ceto daga rundunar da kungiyoyin al'umma, sun kai gawarwakin asibitoci, inda kuma suka gano mutane biyu da suka tsira da ransu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China