Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Harin da aka kai wani masallaci a kudu maso yammacin Pakistan ya yi sanadin mutuwar mutane 14 da jikkatar wasu 20
2020-01-11 17:00:50        cri
Wani hari da aka kai wani masallaci a birnin Quetta na lardin Balochistan dake kudu maso yammacin Pakistan a jiya Juma'a da daddare, ya yi sanadin mutuwar mutane 14 da jikkatar wasu 20.

Babban sufeton 'yan sandan Quetta, Abdul Razzaq Cheema, ya shaidawa Xinhua cewa, wadanda harin ya rutsa da su, ciki har da wani mataimakin sufritandan 'yan sanda, na sallah ne a masallacin a lokacin harin.

Da yake bayyana rahotannin binciken farko-farko ga manema labarai, Ministan cikin gidan lardin, Zia Ullah Langau, ya ce ana tunanin wani dan kunar bakin wake ne ya kai harin daga wajen mallacin. Yana mai cewa an kara tsaurara tsaro a masallatai da sauran wuraren ibada dake lardin.

Kawo yanzu, babu wani mutum ko wata kungiya da ta dauki nauyin harin.

Firaministan Pakistan, Imran Khan, ya yi tir da harin yana mai umartar hukumomin asibiti su ba da kulawa mai inganci ga wadanda suka jikkata. Ya kuma nemi hukumomi masu ruwa da tsaki su gabatar masa rahoto game da lamarin.

Wannan shi ne karo na 2 da aka kai hari birnin cikin kasa da mako 1. Ko a ranar Talatar da ta gabata, wasu mutane 2 sun mutu yayin da wasu 18 suka jikkata, sanadiyyar wani harin bom da aka kai kusa da wata motar jami'an tsaro a birnin na Quetta. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China