Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Pakistan ya gana da ministan wajen kasar Sin
2019-09-09 10:03:40        cri
A jiya Lahadi ne shugaban kasar Pakistan Arif Alvi, ya gana da mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, gami da ministan harkokin wajen kasar, Mista Wang Yi, a Islamabad, fadar mulkin kasar Pakistan.

Yayin ganawar ta su, shugaba Alvi ya ce, Pakistan na kallon kasar Sin a matsayin wata sahihiyar aminiya, wadda za a iya ba ta cikakken imani. Haka kuma ya nuna godiya ga kasar Sin, game da yadda ta dade tana kokarin taimakawa kasar Pakistan a fannoni daban daban.

A cewar shugaban, kasar Pakistan ta ki yarda da duk wani yunkuri na mai da kasar Sin saniyar ware, da kawo cikas ga kokarin kasar na neman raya kanta. Pakistan tana kuma son zurfafa hadin gwiwa ta fuskar yakar ta'addanci tare da kasar Sin, don dakile kungiyar 'yan ta'adda, ciki hadda ETIM da dai sauransu.

A nasa bangare, Wang Yi ya ce, kasar Sin na son hadda hannu tare da Pakistan, don raya wata al'umma mai makomar bai daya a tsakaninsu. Ya ce za a ci gaba da kokarin raya zirin tattalin arziki a tsakanin Sin da Pakistan, don mai da shi wani abun koyi ga sauran ayyukan dake gudana karkashin shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya". (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China