Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mnangagwa: Tawagar kwararrun likitocin kasar Sin ta taimakawa kasar Zimbabwe yakar cutar COVID-19
2020-05-23 15:33:19        cri
Shugaban kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa ya godewa wata tawagar kwararrun likitocin kasar Sin dake kammala aikinta a kasar a jiya Juma'a, inda ya ce a madadin gwamnatinsa, da jama'ar kasar, yana yaba musu bisa gudunmowar da suka samar a fannin taimakawa yakar cutar COVID-19.

Ministan lafiya na kasar Zimbabwe, Obadiah Moyo, ya karanta wasikar da shugaba Mnangagwa ya rubuta a wajen wani taron manema labaru, inda a cikin wasikar, shugaban ya ce likitocin kasar Sin sun gabatar da fasahohin da kasar Sin ta samu a kokarinta na shawo kan cutar COVID-19 ga takwarorinsu na kasar Zimbabwe, lamarin da ya sa jami'an lafiya da likitoci na kasar samun bayanai masu daraja matuka. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China