Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Annobar COVID-19 ba za ta hana ci gaban tattalin arzikin kasar Sin ba
2020-05-20 20:08:26        cri
A wannan mako ne za a kaddamar da tarukan shekara-shekara na majalissun kasar Sin. Bisa la'akari da matsalolin bazuwar cutar COVID-19 a kasashe daban daban, da raunatar cinikin kasa da kasa, da koma bayan da ake samu a kasuwar hada-hadar kudi, yadda haka kasar Sin za ta yi kokarin shawo kan cutar COVID-19, da neman raya tattalin arziki da zaman rayuwar al'umma, lamarin da ya janyo hankalin jama'ar duniya matuka.

Sai dai alkaluman da aka samu sun nuna cewa, ko da yake tana ci gaba da fuskantar jarrabawar annobar COVID-19, amma yanayin samun ci gaba na tattalin arzikin kasar Sin bai canza ba. Don haka kasar Sin na da cikakken karfin zuci wajen haye wahalhalu, da cimma burinta na raya tattalin arzikin da zaman al'umma.

Tun daga lokacin barkewar cutar COVID-19 har zuwa yanzu, bangaren tattalin arzikin kasar Sin ya nuna jajircewa sosai. Sa'an nan bayan da aka samu shawo kan yaduwar cutar a cikin gidan kasar, masana'antu da aikin samar da kayayyaki sun samu farfadowa cikin sauri.

Hakika dukkan alkaluma masu alaka da tattalin arzikin kasar Sin na wadannan watanni 2 sun nuna cewa, tattalin arziki na samun farfadowa matuka. Misali, a watan Afrilun da ya wuce, adadin kudi mai alaka da masana'antun kasar ya karu da kashi 3.9%, idan an kwatanta da makamancin lokaci a bara. Kana yawan darajar kayayyakin da kasar ke fitarwa shi ma ya karu da kashi 8.2% bisa na bara, kuma dukkan wadannan karuwa sun dara yadda aka zata a baya.

Ban da wannan kuma, zaman rayuwar jama'ar kasar Sin shi ma ya kusan komawa matsayinsa kafin bullar cutar COVID-19. Yanzu haka al'ummar kasar suna iya fita waje don sayen kayayyaki, da cin abinci, har ma da yin bulaguro. Tsakanin wasu kwanakin da aka yi wani gajeren hutu, bayan ranar 1 ga watan Mayu, Sinawa kimanin miliyan 115 sun fita yawon shakatawa zuwa sauran wurare. Wannan ma shaida ce dake nuna cewa, annoba ba za ta hana ci gaban tattalin arzikin kasar Sin ba.

Idan an duba wasu sharudda masu zurfi, za a ga cewa, wasu abubuwa masu fifiko da kasar Sin ke da su, irinsu masana'antu, da ma'aikata masu fasaha, dukkansu suna nan. Wannan kari ne kan hidimar sufuri mai inganci, da kayayyakin zirga-zirga, sun kuma tabbatar da karuwar tattalin arzikin kasar cikin wani dogon lokaci mai zuwa.

Haka kuma, kasar Sin na kokarin zurfafa gyare-gyare, da bude kofarta ga kasashen duniya, gami da kirkiro sabbin fasahohi. Dukkan wadannan fannoni za su sa kaimi ga ci gaban tattalin arzikin kasar. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China