Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin dake samun goyon bayan MDD tayi watsi da shiga tattaunawar sulhun Libya
2020-02-19 12:22:53        cri
Gwamnatin Libya dake samun goyon bayan MDD a jiya Talata ta sanar da kauracewa shiga tattaunawar sulhu na hadin gwiwar hukumomin sojojin bangarorin kasar Libyan wanda aka shirya gudanarwa a Geneva, bayan da abokan gabarta wato sojojin dake da sansani a gabashin Libya suka kaddamar da hari kan jirgin ruwan Turkiyya a gabar tekun kasar.

Cikin wata sanarwa da gwamnatin mai samun goyon MDD ta fitar a ranar Talata tace tayi watsi da shiga tattaunawar sojoji ta Geneva, har sai idan bangarorin kasa da kasa sun dauki matakan hukunta laifukan hare haren da sojojin dake gabashin kasar suka kaddamar.

A cewar sanarwar, ofishin shugaban gwamnatin hadin kan kasar ya nanata cewa babu sauran cimma daidaito idan har ba a samu cikakken tsakaita bude wuta ba, idan ba a samar da tabbacin bada kariya ga babban birnin kasar da sauran biranen dake fuskantar barazana ba, kuma idan har ba a tabbatar da maido da mutanen da rikici ya tilastawa kauracewa gidajensu ba.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China