Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Libya ta musanta bullar cutar COVID-19 a kasar
2020-03-09 10:16:39        cri
Ma'aikatar lafiya ta gwamnatin Libya da MDD ke marawa baya, ta musanta jita-jitar cewa an samu bullar cutar COVID-19 a kasar.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar a jiya, ta musanta jita-jitar da wasu tasoshin talabijin da kamfanonin dillancin labarai ke yadawa game da zato ko tabbatar da bullar cutar COVID-19 a kasar.

Wata kafar yada labarai ta kasar, ta ruwaito cewa wasu asibitoci a birnin Tripoli, sun karbi marasa lafiya 2 da ake zaton sun kamu da cutar.

Hukumomi a Libya sun dauki matakan kandagarkin cutar, ciki har da dakunan killace masu cutar a birannen Tripoli da Benghazi dake gabashin kasar, da kuma tsaurara binciken lafiya a filayen jirgin sama da tasoshin ruwa da na kan tudu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China