Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Peter Navarro ya gaza wajen dora wa kasar Sin laifuffuka
2020-04-27 14:17:51        cri


Kwanan nan, wani babban jami'in tsara manufofin cinikayya da sana'ar kere-kere a fadar White House ta Amurka, Peter Navarro ya yi karya da yawa bisa hujjar annobar mashako ta COVID-19, a wani yunkuri na bata sunan kasar Sin. Ana kokarin yada wadannan rade-radi masu jirkita gaskiya ne domin dorawa kasar Sin laifin, gami da wanke gwamnatin Donald Trump daga laifin gazawarsa wajen shawo kan annobar yadda ya kamata.

Hakikanin abubuwa sun tabbatar da cewa, dukkan zargin da Peter Navarro ya yiwa kasar Sin, babu gaskiya a ciki ko kadan.

Na farko, Navarro ya danganta asalin cutar COVID-19 da kasar Sin, har ma ya ce a dakin gwaje-gwaje ne aka kirkiri kwayar cutar.

Asalin kwayar cutar batu ne da ya shafi kimiyya, kuma dole ne a ji ra'ayoyi daga masana da kwararru. Sin kasa ce ta farko da ta bada rahoton bullar cutar COVID-19 ga hukumar lafiya ta duniya wato WHO, amma ba ya nufin ta samo asali daga birnin Wuhan.

Abun lura shi ne, bisa wani sabon rahoton binciken da sashin lafiyar jama'a na gwamnatin gundumar Santa Clara ta jihar California ta Amurka ya bayar, tun a ranar 6 ga watan Fabrairu, an samu rasuwar wani mutum sakamakon cutar COVID-19, wanda kuma bai taba ziyartar wuraren dake fama da cutar ba. Kantoman wurin, Mista Jeffrey V. Smith ya bayyana cewa, al'amarin ya shaida cewa, tun daga watan Janairun bana ne kwayar cutar ta fara yaduwa a yankin San Francisco Bay Area, ko kuma kafin ma lokacin.

Har wa yau, a tsakiyar watan Fabrairu, akwai fitattun masana kimiyya 27 wadanda suka wallafa wata sanarwa a mujallar Lancet, inda suka yi Allah wadai da zancen dake cewa, wai dan Adam ne ya kirkiro kwayar cutar COVID-19. Har wa yau, mai magana da yawun hukumar WHO Fadela Chaib ta kuma jaddada cewa, dukkan shaidu na nuna cewa, kwayar cutar ta samo asali daga jikin dabba, ba wai a dakin gwaji ne dan Adam ya kirkire ta ba.

Na biyu, Peter Navarro ya ce, wai kasar Sin ta boye yanayin cutar bisa kariyar WHO. Amma gaskiyar abun shi ne, tun daga ranar 3 ga watan Janairu, Sin ta soma bada rahotanni game da yanayin yaduwar cutar ga WHO da Amurka, da sauran wasu kasashe da kungiyoyin shiyya-shiyya. Bayan kwana biyu kacal wato 5 ga watan Janairun, WHO ta gargadi duk fadin duniya game da bullar wani sabon nau'in cutar numfashi.

Dadin dadawa, wani rahoton da jaridar Washington Post ta ruwaito kwanan nan ya ce, wasu Amurkawa dake aiki a ofishin WHO dake Geneva, sun taba aikawa gwamnatin Trump sabbin bayanai game da annobar COVID-19.

Hakan ya nuna cewa, gwamnatin Trump ta yi biris da gargadin da aka yi mata, abun da ya sa ta gaza wajen shawo kan yaduwar cutar yadda ya kamata. Kamar yadda jaridar Washington Post ta ce, bayan kwanaki 70, gwamnatin Trump ta fara daukar matakai domin dakile yaduwar cutar a kasar.

Abu na uku shi ne, Peter Navarro ya bayyana cewa, wai mutanen kasar Sin suna baza kwayar cutar, al'amarin da ya tada rikici da rura wutar kiyayya ta hanyar yin kabilanci.

Kwayar cutar ba ta san iyaka ko kabila ba. Al'ummar kasar Sin su ma suna jin radadi sosai sakamakon cutar, amma shi Peter Navarro ya ayyana mutanen kasar Sin a matsayin wadanda suka kawo illar cutar. A halin yanzu, yaduwar annobar a Amurka ta sa ana kara nunawa 'yan asalin Asiya wariya da bambanci. Kuma irin wannan zancen kabilanci da Navarro ya yi, zai tsananta halin da 'yan asalin Asiya ke ciki, da kara jefa su cikin hadari.

Hakikanin gaskiya, kasar Sin na daukar managartan matakai daga fannoni daban-daban domin kandagarkin yaduwar cutar, ciki har da takaita zirga-zirgar al'umma, matakin da ya taka birki ga yaduwar cutar a sauran kasashe, da yankuna na tsawon mako biyu zuwa uku.

Na hudu wato na karshe, Peter Navarro ya zargi kasar Sin da tattara kayayyakin kare kai domin samun riba mai tsoka, abun da ya zama babbar karya. Akasin haka, bangarori daban-daban na kasar Sin na gudanar da hadin-gwiwa tare da sauran kasashe domin taimakawa ayyukan yaki da annobar a duk fadin duniya baki daya.

Alkaluman sun yi nuni da cewa, tun daga ranar 1 ga watan Maris zuwa ranar 17 ga watan Afrilu, kasar Sin ta samarwa Amurka abun rufe baki da hanci sama da biliyan 1.8, da safar hannu miliyan 258, da rigunan kare kai sama da miliyan 29, da kuma tabaraun kariya fiye da miliyan 3, da kuma injunan taimakawa numfashi masu tarin yawa.

Amma ita Amurka ba ta samar da taimako takameme ga ayyukan dakile yaduwar cutar na kasa da kasa ba, har ma ta kwace abun rufe baki da hanci da aka yi niyyar jigilarsu zuwa kasar Jamus, ta kuma yi umarni ga kamfanin 3M ya dakatar da fitar da abun rufe baki da hancin zuwa kasar Kanada, da sauran wasu kasashen dake Latin Amurka.

Yanzu Amurka na fuskantar babbar barazanar yaduwar cutar. Irin 'yan siyasar kasar kamar shi Peter Navarro, kamata ya yi su san cewa, kwayar cutar ita ce ke kiyayya ga Amurka, ba kasar Sin ba. Dole ne su dauki managartan matakai domin ceto al'ummar kasar a maimakon yunkurin yada rade-radi game da kasar Sin.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China