Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta ba da ikon wallafa wasu litattafai game da yaki da cutar COVID-19 ga Iran
2020-03-04 14:02:29        cri

A kwanakin baya bayan nan, ana ci gaba da fuskantar yaduwar cutar COVID-19 a kasar Iran, don gane da haka ne kuma, wasu kamfanonin wallafa litattafai na kasar Sin, suka ba da izinin wallafa litattafansu, game da yaki da cutar COVID-19 ga kasar.

Tashar yanar gizo ta aikin fassara da nazarin al'adun kasar Sin, wani dandali ne dake taimakawa masu karatu da masu kallo na kasashen duniya, wajen fahimtar al'adun Sin, da fassara, ko cin gajiyar su. Ta wannan dandali, an sa kaimi ga shigar da litattafai uku na Sin game da kandagarki da yaki da cutar COVID-19, a cikin kasuwar kasar Iran. Litattafan su ne "Forfesa Zhang Wenhong ya koyar da dabarun maganin cutar COVID-19", da "Zane-zane game da magancewa da yaki da cutar COVID-19", da kuma "Dabarun maganin cutar COVID-19".

Shugaba mai kula da wannan aiki na tashar yanar gizon Xu Donghao ta yi bayani da cewa, an shafe kasa da mako daya wajen ba da ikon wallafawa, da fassara wasu abubuwan dake cikin litattafan uku ga kasar Iran. Don taimakawa jama'ar kasar Iran wajen tinkarar cutar COVID-19, wasu kamfanonin wallafa litattafai na kasar Sin, sun ba da ikon wallafa litattafai game da wannan fanni kyauta ga kasar Iran. Xu Donghao ta yi bayani game da yanayin tattauna hadin gwiwa tare da bangaren wallafa litattafai na kasar Iran a kwanakin baya. Ta ce,  

"A kwanakin baya, an kara samun yaduwar cutar COVID-19 a kasar Iran, sai na tambayi wani mawallafin kasar ko yana bukatar wasu litattafan magance yaduwar cutar, na ce Sin tana tinkarar yaki da cutar, muna da fasahohin tinkarar cutar. Sai dai ya ce yana bukatar wasu litattafan magance cutar, daga baya na rubuta bukatun sa a kan shafin mu, kamfanonin wallafa litattafai na Sin, da dama suna son biyan bukatun sa. Bangarorin biyu sun gama zabar litattafai cikin kwanaki hudu kacal, kuma kawo yanzu, an riga an gama fassara daya daga cikin su. Wannan ya zama misali na hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Iran, kan wallafa litattafai cikin sauri. Don sa kaimi ga karin jama'ar kasar Iran, game da yadda wadannan ilmin magance cutar, sun kuma dauki matakan wallafa litattafai ta yanar gizo, jama'a suna iya karanta su ta yanar gizo ba tare da biyan kudi ba."

Kamfanin wallafa litattafai na kimiyya da fasaha na birnin Shanghai, yana da ikon wallafa littafin "Forfesa Zhang Wenhong ya koyar da dabarun maganin cutar COVID-19", ya zuwa yanzu, an riga an gama fassara shi ta harshen Farisa. Mataimakin babban editan kamfanin Zhang Chen ya bayyana cewa, forfesa Zhang Wenhong shi ne mashahurin masanin magance cututtuka dake iya yaduwa a tsakanin dan Adam a kasar Sin, kawo yanzu, an riga an wallafa wannan littafi a kasar Sin fiye da dubu 900, wanda ya kasance littafi mafi karbuwa a tsakanin jama'ar birnin Shanghai, yana fatan wannan littafi zai taimakawa jama'ar kasar Iran wajen magance cutar. Ya ce,

"Mun san Iran za ta gabatarwa al'ummun kasarta litattafan kyauta, a don haka muna son ba da ikon wallafa wannan littafi a kyauta. Mun tambayi forfesa Zhang Wenhong, shi ma ya amince. Muna fatan wannan littafi zai biya bukatun masu karatu na kasar Iran, da taimaka musu wajen dakile cutar ta hanyar kimiyya."

Kamfanoni biyu na wallafa litattafai dake birnin Tianjin, sun yi hadin gwiwa wajen wallafa littafin "Zane-zane game da magance da yaki da cutar COVID-19", cikin yaruka biyu, wato na Sinanci da na Turanci. An wallafa littafin na Turanci, don samar da hidima ga 'yan kasashen ketare dake zaune a birnin Tianjin, da ma duk fadin kasar Sin, wajen magance cutar. Mataimakiyar manajan kamfanin wallafa litattafai na Tianjin Ji Xiurong ta bayyana cewa,

"Yaki da wannan cuta yana shafar dukkan dan Adam, ya kamata mu yi kokari tare, mu tsai da kudurin ba da ikon wallafa wannan littafi ga Iran, don nuna goyon baya gare ta wajen magancewa da yaki da cutar."

Ali Khakbazan shi ne shugaban wani kamfanin wallafa litattafan yara na kasar Iran, kamfaninsa ya zabi litattafai biyu, wato "Zane-zane game da magancewa, da yaki da cutar COVID-19", da kuma "Dabarun maganin cutar COVID-19". Ya ce, a halin yanzu babu irin wadannan litattafai a kasar Iran, wadannan litattafai biyu na kasar Sin, suna da saukin fahimta. Ya ce,

"Cutar COVID-19 tana shafar dukkan duniya baki daya, kuma yanzu ana fama da cutar mai tsanani a kasar Iran, don haka ya kamata kowa da kowa ya taka rawa wajen magancewa da yaki da cutar. Mun zabi litattafai biyu daga cikin litattafan hudu da Sin ta gabatar, wadanda suke da saukin fahimta. Za mu fassara su, da mika su zuwa ma'aikatar kiwon lafiya don yin bincike, sannan mu mika su ga hukumomin kiwon lafiya, da jami'o'i, da sauran hukumomin da abin ya shafa, don wallafa su ta yanar gizo ga jama'ar kasar." (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China