Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Iran: Sin babbar kasa ce mai sauke nauyin dake wuyanta
2020-03-06 12:25:08        cri

A 'yan kwanakin da suka gabata, kasar Sin ta samu wasu sakamako a bayyane, wajen shawo kan annobar cutar numfashi ta COVID-19, a sa'i daya kuma, tana daukar matakai a jere, don farfado da tattalin arziki bisa sharadin tabbatar da tsaron jama'a. Game da hakan, mashahurin mai yin sharhi kan harkokin kafofin watsa labarai na kasar Iran Bobby Naderi ya zanta da wakilin babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG a takaice, inda ya bayyana cewa, hakikanin abubuwa sun gaskanta cewa, matakan da kasar Sin ta dauka domin dakile annobar sun taka rawa matuka, haka kuma sun samar da fasahohi ga sauran kasashen duniya, yayin da suke kokarin shawo kan annobar dake bazuwa a kasashen su.

Mashahurin mai yin sharhi kan harkokin kafofin watsa labarai na Iran Bobby Naderi ya gayawa wakilin babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG a takaice, cewa hakikanin abubuwa sun gaskanta cewa, matakan da kasar Sin ta dauka domin dakile annobar sun taka rawa matuka, haka kuma sun samar da fasahohi ga sauran kasashen duniya yayin da suke kokarin shawo kan annobar dake bazuwa a kasashensu, kana kokarin da kasar Sin take wajen farfado da tattalin arzikin kasar shi ma ya nuna cewa, kasar Sin babbar kasa ce wadda ke sauke nauyin dake wuyan ta, dalilin da ya sa haka shi ne, domin farfado da tattalin arzikin kasar Sin zai ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya, idan kamfanonin dake kasar Sin ba su koma bakin aikinsu a kan lokaci ba, to hakan zai kawo illa ga tattalin arzikin duniya.

Naderi yana ganin cewa, matakan da kasar Sin ta dauka a fannin dakile annobar numfashi ta COVID-19 suna da amfani matuka, haka kuma sun samar da fasahohi ga sauran kasashen duniya yayin da suke kokarin shawo kan cutar, misali an samar da bayanan da abin ya shafa a fili cikin lokaci, kuma an dauki matakai ba tare da bata lokaci ba, yana mai cewa, "Matakan da kasar Sin ta dauka wajen dakile annobar, sun samar da abin koyi ga sauran kasashen duniya, har ma suna koyon fasahohin kasar Sin, yayin da suke kokarin shawo kan annobar, saboda matakan kasar Sin suna da amfani matuka wajen hana yaduwar annobar. Ana iya cewa, kasar Sin babbar kasa ce mai sauke nauyin dake wuyanta, a harkokin kasa da kasa, a don haka ya dace sauran kasashen duniya su koyi fasahohin kasar Sin, su samar da bayanai a fili cikin lokaci, haka kuma su dauki matakai ba tare da bata lokaci ba."

Naderi ya kara da cewa, yayin da kasar Sin ta samu sakamakon shawo kan annobar, ta kuma dauki matakai a jere domin farfado da tattalin arzikin ta, wannan lamarin ba ma kawai yana da babbar ma'ana ga ci gaban tattalin arzikin kasar kan ta ba ne, har ma zai ingiza karuwar tattalin arzikin duniya, kuma kokarin da kasar Sin take yi shi ma ya nuna cewa, kasar Sin babbar kasa ce wadda ke sauke nauyi bisa wuyanta, a fannin tattalin arziki. Ya ce, "Bisa matsayin ta na kasa mafi saurin ci gaban tattalin arziki ta biyu a duniya, kasar Sin tana samun ci gaba ne tare da sauran kasashen duniya, wato ci gaban kasar Sin yana shafar ci gaban sauran kasashen duniya, yanzu haka kasar Sin tana sanya kokari matuka domin farfado da tattalin arzikin ta wanda ya gamu da matsala a sanadin bazuwar annobar cutar numfashi ta COVID-19 a cikin watanni uku na farkon bana, amma muna cike da imani kan makomar ci gaban tattalin arzikin kasar ta Sin a cikin watanni masu zuwa."

Yayin zantawar ta su, Naderi ya soki wasu kafofin watsa labaran kasashen yamma bisa zargin da suka yiwa kasar Sin, wato ta nemi gafara daga wajen sauran kasashen duniya saboda barkewar annobar, inda ya bayyana cewa, bayan barkewar annobar, kasar Sin ta dauki matakai a jere domin hana yaduwar ta, kuma bai dace ba kafofin watsa labaran wasu kasashen yamma su kasa kula da kokarin da kasar Sin ta yi, yana mai cewa, "Bai dace ba a bukaci kasar Sin ta nemi afuwa, saboda kwayar cuta tana shafar daukacin bil Adam a fadin duniya, kuma babu bambancin kabila, ko addini, ko asalin kasa dake gaban ta. Hakika ba ma kawai kasar Sin ta dauki matakai a kan lokaci ba ne, har ma ta yi musanyar bayanai da fasahohin da ta samu tare da sauran kasashen duniya wajen dakile annobar. Cutar COVID-19 barazanar lafiyar jama'a ce da daukacin kasashen duniya ke fuskantar, ya kamata mu hada kai domin ganin bayanta tun da wurwuri, saboda daukacin dan Adam suna cikin jirgin ruwa guda daya ne, idan ya kife, kowa da kowa zai gamu da matsala."

Haka zalika, Naderi shi ya kuma jinjinawa tallafin da kasar Sin, da hukumar lafiya ta duniya, da sauran kungiyoyin kasa da kasa suke samarwa kasar Iran wajen dakile annobar. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China