Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WFP ya yi gargadi game da matsalar yunwa da za ta addabi duniya baya ga COVID-19
2020-04-22 11:08:26        cri
Babban darektan shirin samar da abinci na duniya (WFP) David Beasley, ya yi gargadi game da yadda yunwa za ta addabi sassan duniya, yayin da ake fama da annobar COVID-19.

Ya shaidawa taron kwamitin sulhu na MDD ta kafar bidiyo cewa, ya fadawa shugabannin kasashen duniya yayin tattaunawar da suka yi watanni da dama da suka gabata, kafin cutar COVID-19 ta zama wani batu na daban cewa, a shekarar 2020 da muke ciki, za a fuskanci mummunan matsalar jin kai da ba a taba gani irinta ba, tun a lokacin yakin duniya na biyu saboda wasu dalilai.

Ya shaidawa zaman muhawarar kwamitin sulhu kan yadda za a kare fararen hula da yunwa ta shafa sakamakon rikici cewa, a yau, yayin da ake fama da COVID-19, "Ina son in jaddada cewa, ba kawai muna fama da annobar lafiya da ta shafi duniya baki daya ba, har ma ta haifar matsalar jin kai."

Jami'in ya ba da misali da wani sabon rahoto da aka fitar game da matsalar abinci da duniya ke fuskanta, inda ya nuna cewa, kimanin mutane miliyan 821 ne suke kwana da yunwa a duniya. Akwai kuma karin mutane miliyan 135 dake fama da matsalar yanayi na yunwa ko fiye da haka.

Wani sharhin da shirin na WFP ya fitar, ya nuna cewa, a sakamakon annobar COVID-19, ya zuwa karshen shekarar 2020, wasu karin mutane miliyan 130 za su iya fadawa kangin yunwa. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China