Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Africa CDC: Yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Afirka ya karu zuwa 23,505
2020-04-22 11:02:07        cri
Cibiyar kandagarki da hana yaduwar cututtuka ta Afirka (Africa CDC) ta bayyana cewa, ya zuwa jiya Talata, yawan wadanda cutar COVID-19 ta halaka a nahiyar Afirka ya kai 1,159, kana yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar, ya karu zuwa 23,505.

Cibiyar, kwararriyar hukumar kungiyar tarayyar Afirka (AU) mai mambobin kasashe 55, ta bayyana cikin rahoton baya-bayan da ta fitar game da yanayin cutar a yau Laraba cewa, yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a sassan nahiyar ya karu daga 22,513 a ranar Litinin zuwa 23,505 a ranar Talata. Yanzu haka kuma, cutar ta yadu zuwa kasashe 52 na nahiyar.

Bugu da kari, alkaluman da cibiyar ta fitar, sun nuna cewa, yayin da cutar ke yaduwa a sassan nahiyar, kasashen da cutar ta fi shafa, sun hada da Masar mai mutane 3,333, Afirka ta kudu mai mutane 3,300, Aljeriya mai mutane 2,718 sai kasar Morocco mai mutane 3,064.

Cibiyar Africa CDC, ta kuma bayyana cewa, yawan mutanen da cutar ta halaka a sassan nahiyar ya zuwa ranar Litinin ya kai 1,126, yayin da adadin ya karu zuwa 1,158 ya zuwa ranar Talata da rana. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China