Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: COVID-19 na da asali da dabba
2020-04-22 09:47:22        cri
Mai magana da yawun hukumar lafiya ta duniya WHO Fadela Chaib, ta bayyana a jiya Talata cewa, dukkan shaidu sun yanke shawarar ce, cutar numfashi ta COVID-19 na da asali da dabba, kuma ba wani ne ya kirkiro ko ya samar da ita a dakin bincike ko a wani wuri ba.

Da take yiwa manema labarai karin haske yayin taron da aka shirya ta kafar bidiyo, Fadela ta ce, "WHO ta fada, kamar yadda na bayyana cewa, a matsayinta na hukuma mai kwarewa a fannin kimiya, muna tunanin cutar ta sami asali daga dabba," watakila akwai ta a jikin jemaga, amma har yanzu ba a gano yadda dan-Adam ke daukar cutar daga jikin Jemagen ba.

Ta kara da cewa, hakika akwai dabbar dake yada wannan cuta daga Jemagu zuwa jikin dan-Adam. A don haka, ta yi alkawarin cewa, WHO tana maraba da dukkan kasashe, da su goyi bayan kokarin da ake yi na gano asalin kwayar cutar, tana mai cewa, kungiyoyi da dama, ciki har da masanan kasar Sin, suna can suna kokarin gano asalin wannan kwayar cutar. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China