Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin kwayoyin halitta na Birtaniya: an samu yawancin kwayar cuta ta COVID 19 ta matakin farko a Amurka
2020-04-13 11:21:03        cri

Masanin kwayoyin halitta dake jami'ar Cambridge Farfesa Peter Forster, ya bayyana a kwanakin baya cewa, an gano yawancin kwayar cuta numfashi ta COVID 19 a mataki na farko, a jikin wadanda suka kamu da cutar a Amurka, don haka birnin Wuhan ba shi ne wurin da aka samu asalin cutar ba.

A cewarsa, wannan kwayar cuta ta sauya halitta ne har sau biyu, kuma lokacin sauye-sauye karo na biyu da ta yi, ya ragu da kaso 50% idan an kwatanta da karon ta na farko.

Game da lokacin gabatar da allurar rigakafin cutar kuwa, Forster ya ce, ko da yake shi ba masani ne a wannan fanni ba, amma ya yi imanin cewa, za a gabatar da ita cikin shekara daya, ko shekara daya da rabi. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China