Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Africa CDC: Yawan wadanda suka kamu da COVID-19 a Afirka ya kai 10,692
2020-04-09 10:47:05        cri

Cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Afirka (Afirca CDC) ta bayyana cewa, ya zuwa jiya Laraba, yawan mutanen da cutar numfashi ta COVID-19 dake yaduwa a nahiyar ta halaka, ya haura 535, yayin da adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ya dara 10,692 a kasashe 52 na nahiyar.

Bugu da kari, alkaluman da cibiyar ta fitar sun nuna cewa, kasashen da annobar ta shafa, sun hada da Afirka ta kudu da Aljeriya, da Masar da kasar Morocco.

Tun a ranar 27 ga watan Janairun wannan shekara ce, kungiyar tarayyar Afirka ta hannun cibiyar Africa CDC, ta farfado da cibiyar ayyukan ta na gaggawa, da tsarin sanya ido(IMS) kan barkewar cutar ta COVID-19.

Haka kuma, cibiyar Africa CDC, ta bullo da kashi na uku na tsarin sanya ido, shirin da zai gudana daga ranar 16 ga watan Maris zuwa 15 ga watan Afrilu. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China