Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Alakanta Fasahar 5G Da COVID-19: Rainin Hankali Ko Hassada?
2020-04-06 21:03:14        cri

Daga abubuwan da suka fi daukar hankalin jama'a a wannan makon akwai batun da ake ta yamadidi a kai na alakanta bazuwar cutar Kwarona da fasahar sadarwar 5G. Ba a Nijeriya ba kawai, ba Afirka ba a kusan dukkan kasashen duniya musamman na yammacin Turai abin ya ta'azzara, inda ake yawo da wasu hotunan bidiyo na wasu matasa a Turai suna kayar da turakun fasahar ko kuma banka musu wuta.

A daya daga cikin bidiyon da na gani, an daura wa wani turken fasahar na 5G igiya, wasu sun kama ta kusurwar yamma, wasu ta gabas suka dage da karfin cin tuwonsu sai da suka kai shi kasa ya fadi rikica!

Da farko, a lokacin da wani abokina ya aiko mun da bidiyon ta manhajar Whatsapp na dauka wasan kwaiwayo ne, amma da na kasa kunne da kyau na ji bayanan da ake yi na cewa fasahar sadarwar 5G na taimakawa wajen yada cutar Kwarona sai tunanina ya zurfafa.

Abu na farko shi ne, mece ce alakarsu, hanyar jirgi daban, ta mota daban. 5G fasaha ce ta maganadisu, cutar Kwarona kuma kwayar halitta ce daga cikin halittun da ido na kan mutum ya yi kadan ya yi tsinkaye a kai, ko da na'ura ma sai an yi da gaske ake iya gani. Ko da yake, fasahar Dan Adam a kullum yaumin tana kara samun ci gaba, amma kuma ga masu hankali suna da ma'auni mai kyau wadda ko da ta ishara aka isar da sako sun fahimta ba sai an fito fili ba. Don haka ga irin wadannan mutanen rabe zare da abawa ba wani abu ne da yake gagarar kundila ba.

Tunanin da ake yi mai zurfi game da wannan lamari ya nausa da ni zuwa tashar tarihin ziyarar aikin da muka kai kasar Sin tare da wasu abokan aiki mu biyar daga Kamfanin Jaridun LEADERSHIP a shekarar 2018, ta karshen watan Afrilu. Kamfanin Huawei wanda ya samar da fasahar sadarwar mai karfin 5G yana daya daga cikin muhimman wuraren da muka ziyarta a Shanghai.

A wannan lokacin, kamfanin yana kokarin ganin ya kara bunkasa fasahar karfin sadarwa daga 4G zuwa 5G har ma ya kammala aikin kashi na farko. Daga abin da aka bayyana mana, kamfanin ya ce idan ya kammala aikin samar da fasahar ta 5G ba sai ya sauya gangar jikin na'urorin 4G ba, ya samar da wani jirgi mara matuki na fasaha da zai tashi zuwa manyan tashoshin fasaharsa domin ya sauya fasahar 4G take-yanke zuwa 5G. Wannan abin birgewa ne kwarai da gaske, ko ba komai a matsayinmu na Bani Adam ya dace mu yi murna da samun wannan fasaha a doron kasa.

Bayan kammala aikin samar da fasahar 5G da kuma fara amfani da ita, kamfanonin sadarwa har da namu na Afirka sun yaba da abin, har ma Kamfanin Layin MTN ya nuna aniyarsa ta gwajin fasahar a shekarar bara, bayan ya samu amincewar Hukumar Sadarwa ta Kasa (Nigeria Communication Commission) a cikin watan Nuwamba. Kamar yadda ake iya gane yadda fasahar 5G ta fi ta 4G saurin aika sako, haka ma abin yake kasancewa a tsakanin 4G da 5G.

Gaskiya a fade ta komai dacinta, duk masu bibiyar al'amuran yau da kullum da siyasar duniya sun san irin farfagandar da Yammacin Turai ke yi ta bata wasu hikimomi da ci gaban da ake samu a wasu kasashen da ba nasu ba. Saboda haka ba abin mamaki ba ne don an samu farfagandar bata 5G daga gare su, amma abin mamakin shi ne: imanin da wasu mutane suka yi na cewa fasahar tana yada cutar Kwarona.

Kamar yadda na yi tsinkaye a rubutun da wani Lauyan Nijeriya kuma mai fashin bakin al'amuran yau da kullum, Barista Frank Tietie ya yi a turakarsa na shafukan walwala, daga Babban Birnin Tarayya Abuja, a kan "Kudirin 'Yan Kungiyar Asirin Duniya (Dujjalawa) da Bukatar Warware Matsaloli A Mizanin Fahimtar Afirka", ya bayyana wani tsohon mai gabatar da shirye-shirye a Hukumar BBC, David Icke a matsayin wanda ya ta'allaka cutar Kwarona da 5G.

Shi wannan mutumin kamar yadda Lauyan ya yi bayani a kansa, ya kware wajen fito da nazari a kan munakisa wanda yake gudanar da kwakkwaran bincike a kai, sai dai sakamakon binciken nasa kan zama kame-kame wajen kammalawa. Don haka cikin sauki ana iya yin watsi da batutuwansa musamman ma abin da ya shafi cutar Kwarona.

Icke ya yi amanna da cewa cutar Kwarona (COVID-19) kirkirarta aka yi (ba halitta ba ce), an kera alamominta ce daga tarin gubar da ke fitowa lokacin da ake amfani da 5G, kuma ya sake cewa alamominta suna da alaka da alamomin mura. Sannan mutanen da ke zuwa domin a yi musu gwajin ko sun kamu da cutar ana yada musu ita; daga bisani su kamu da matsanancin rashin lafiya watakila ma abin ya kai su ga mutuwa. Don haka ya shawarci mutane cewa kar su yarda su je a gwada su. Ya yi imanin cewa duk wanda ya nuna kamuwa da alamomin da aka ta'alla da cutar ta Kwarona; zai warke idan aka yi masa maganin mura kamar yadda ya kamata.

Hadarin bayanan Mista Icke yana da yawa, domin akwai mutanen da ake ganin suna da kima da daraja da ya zama musu abin kafa hujja bayan sun yi imani da ayyukansa. Ko a kwanan baya, David Icke ya ci kasuwarsa a lokacin da ya bayyana a gidan Talabijin na LondonReal, ya yi bayanin cewa mutane su bibiyi nazarin da ya yi a kan kashi 1 na yawan mutanen duniya ne kacal suke juya duniya bakidaya.

Galibin hujjojin da Icke yake gabatarwa a ayyukansa ba su da madafa ko madogara da za su tabbatar da sahihancinsu. Kuma saboda watakila tsoron makirci ne, hatta mutanen da ake ganin hamshakai ne sun mallaki dukkan abubuwan da za su iya yi masa raddi sai ka ji su tsit!

Ire-iren mutanen su ne Bill Gates wanda Icke ya yi ikirarin cewa magungunan rigakafin da yake bayarwa tallafi ga al'ummar duniya suna haddasa wa mutane rashin lafiyar da za su tilasta musu dogaro da sayen magungunan da manyan kamfanonin harhada magunguna ke sarrafawa. Shi ma hamshakin nan na Amurka, Mista George Soros, Icke bai bar bar shi ba, ya shafa masa cewa yana shirya tuggun hargitsa duniya da lalata dan adamtaka.

Haka nan, Icke ya taba cin mutuncin matashin hamshakin nan, Mark Zuckerberg inda ya bayyana shi a matsayin karamin yaro da manya ke amfani da shi domin cimma muguwar boyayyiyar manufarsu.

Wadan nan kadan ne daga cikin misalan abubuwan da David Icke yake yi domin wawantar da al'umma. Idan ya bushi isaka, sai ya yi wa abu fenti ya ce yana da kyau, idan kuma ba ya son wani abu, ya shafa masa bakin fenti.

Saboda haka, Barista Frank Tietie ya yi kira ga mahukuntanmu na Afirka lallai ya zama wajibi duk irin matsalar da ta taso a duniya kar mu bi ribibi, mu tsaya mu yi nazarin matsalar da kuma samar da mafita a bisa mizaninmu na fahimtar Afirka.

Shi ya sa matakin da Hukumar Kula da Sadarwa ta Kasa (Nigerian Communications Commission) ta dauka a Litinin din nan na karyata alaka tsakanin cutar Kwarona da fasahar 5G, abu ne da ya dace kwarai kuma abin a yaba.

Duk da kasancewar hukumar ba ta bayar da damar kawo fasahar cikin kasa ba, amma kuma ta yi gaba-gaba wajen karyata wannan farfaganda domin fayyace wa al'umma gaskiya.

Sai dai duk da haka, akwai jan aiki a gaban Kasar Sin da kuma musamman kamfanin Huawei da ya samar da fasahar ta 5G na wayar da kan al'ummar da suka amince da farfagandar ta masu neman yi wa wannan ci gaba kafar ungulu, wanda mutane da dama da suke da ma'auni na ilimi ke tambayar cewa, shin wannan farfaganda 'rainin hankali ce ko hassada?' (Abdulrazaq Yahuza Jere)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China