Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ko fasahar 5G ce ta haddasa cutar COVID-19?
2020-04-06 20:44:55        cri

A 'yan kwanakin baya, an kone hasumiyoyin sadarwa masu watsa sakwanni ta fasahar 5G guda 2, da aka kafa a Birmingham da Merseyside na kasar Birtaniya, sabo da wani zargi da ake yi cewa, annobar COVID-19 ta yadu ne sakamakon amfani da turakun na 5G.

Game da irin wannan maganar dake karyata ilmin kimiyya, a ranar 4 ga watan Afrilu, Mr. Michael Gove, ministan ilmi na kasar Burtaniya ya fusata, yana mai cewa, "wannan maganar banza ce mai hadari, kuma maganar alakanta yaduwar kwayar cutar COVID-19 da fasahar 5G, ta kasance kamar wani makirci ne."

Mr. Stephen H. Powis, babban jami'i mai sa ido kan aikin jinya na Ingila karkashin tsarin ba da hidimar jinya na kasar Birtaniya ko NHS a takaice, ya yi suka da cewa, irin wannan "magana" labari ne na karya kawai. Amma har yanzu, akwai wasu mutanen da suke amincewa da irin wannan "magana" kwarai. Alal misali, Amir Kahan, tsohon "sarkin dambe" na kasar Birtaniya, wanda ya taba cin gasannin WBA da IBF da WBO gaba daya, ya amince da maganar, har ma ya watsa ra'ayinsa a shafinsa dake Instagram yana cewa, cutar numfashi ta COVID-19 ta barke a kasar Birtaniya ne, sakamakon yadda gwamnatin Birtaniya ta gina turakun watsa kafar sadarwa ta 5G, domin tana son kayyade yawan al'ummar kasar, da kuma hallaka tsofaffi. Ya kara da cewa, "A gani na, cutar numfashi ta COVID-19 ba daga kasar Sin ta fito ba. Dalilin da ya sa ake kamuwa da cutar a duk fadin duniya shi ne, ana gwada fasahar 5G."

Amma abun tambaya a nan shi ne, shin kamar yadda Amir Kahan ya fadi, fasahar 5G ce ta haddasa cutar COVID-19? Idan muna son amsa wannan tambaya, da farko dai, bari mu san mene ne 5G.

A cikin shekaru 30 da suka gabata, fasahohin sadarwa na tafi da gidanka, sun samu ci gaba daga 1G zuwa 2G, sannan daga 2G zuwa 3G, daga bayam daga 3G zuwa 4G, har ma 5G da ake ginawa a yanzu a wasu kasashen duniya. A nan gaba, kamar nan da shekaru 5 ko 10 masu zuwa, za a kirkiro fasahar 6G ta sadarwa, sabo da yanzu wasu kasashen duniya sun riga sun fara nazarin fasahar 6G. Ma'anar "G" ita ce farkon baki na "Generation" cikin harshen Turanci. Bisa fasahar 5G, za a iya sauke wani fim na mintuna 90 ko 120 cikin dakika 1 ko 2 ba tare da jinkiri ba. Har ma motoci za su iya gudu da kansu a titi bisa fasahar 5G.

Kamar yadda ake amfani da fasahohin 1G da 2G da 3G da 4G yanzu, ana bukatar gina dimbin husumiyoyi ko turakun da za su dauki na'urorin watsa alamunsu a duk fadin kasa. Babu shakka, a lokacin da na'urorin watsa alamun sadarwa suke aiki, suna kuma watsa "radiation" kamar yadda duniyarmu, ko tsawa, ko kwamfuta, ko akwatin talibijin, ko na'urar bushe gashin kai, da sauran na'urori masu aiki da wutar lantarki suke yi a kullum. Sabo da haka, wasu suna yada maganganu a cikin "Moment" wato sakwanin da kan bayyana a shafukan sada zumunta cewa, Shi sinadarin "radiation" da na'urorin watsa alamun sadarwar 5G yake fitarwa yana da yawan gaske, har ma zai iya lahanta lafiyar dan Adam.

Amma masana wadanda suka kirkiro fasahar 5G sun ce, yawan sinadarin da na'urar bushe gashin kai take yadawa, na kan kaiwa microwatts 100 a kowane murabba'in centimita. Sannan yawan sinadarin da na'urar dafa abinci mai aiki da wutar lantarki take yadawa, ya kai microwatts 580 a kowane murabba'in centimita. Amma bisa ma'aunin da kasar Sin ta tsara, yanzu, yawan sinadarin radiation da kowace husumiya ko turkin yada alamun sadarwa ta 5G zai fitar, ba zai iya wuce microwatts 40 a kowace centimita ba. Ke nan ana iya gane cewa, yawan sinadarin radiation da na'urar yada alamun sadarwar 5G take yadawa dan kalilan ne, ta yadda ba zai yiwu ya lahanta lafiyar kowane mutum ba.

Kamar yadda Mr. Stephen H. Powis, babban jami'i mai sa ido kan aikin jinya na Ingila karkashin tsarin ba da hidimar jinya na kasar Burtaniya NHS ya bayyana, "maganar wai fasahar 5G na lahanta lafiyar mutum, ta kasance kamar shara ce, ba ta da ma'ana ko kadan, kuma mugun labarin jabu ne." "A hakika dai, turkin sadarwa na wayoyin tarho na tafi da gidanka, na da muhimmanci matuka ga dukkan mutane, musamman ga wadanda suke aikin ba da hidima, da jami'an kiwon lafiya. Ina jin haushi matuka, kuma ina kyamar irin wannan laifi na lalata aikin sadarwa na more rayuwar jama'a, musamman a wannan muhimmin lokaci da ake yunkurin dakile annobar da ta barke ba zato ba tsammani."

Kamfanin Vodafone, wato kamfanin ba da hidimar wayar tarho ta tafi da gidanka mafi girma na biyu a duk fadin duniya, shi ma ya bayyana cewa, irin wannan magana ta riga ta kawo illa ga tsaron kan kasar Birtaniya.

Annobar COVID-19 abokiyar gaba ce ta daukacin bil Adama. Amma fasahar sadarwa ta 5G, fasahar sadarwa ce ta zamani, wadda za ta kawo alheri ga daukacin bil Adama. Duk haka ya kamata kowa ya kara koyon ilmin kimiyya, ta yadda zai iya bambamce jita-jita da abun da yake gaskiya.

Muna da imanin cewa, idan dukkanmu mun dakile annobar bisa ilmin kimiyya, to kuwa tabbas za mu iya shawo kan annobar kamar yadda ake fata nan gaba ba da dadewa ba.(Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China