Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a duniya ya zarta miliyan 1.1
2020-04-04 15:39:27        cri

A yau Asabar, Jami'ar Johns Hopkins ta Amurka, ta fitar da sabbin alkaluman kididdiga na adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19, inda suka nuna cewa, adadin ya riga ya zarta miliyan daya da dubu 100.

Alkaluman sun nuna cewa, ya zuwa yau da misalin karfe 1 na dare agogon gabashin Amurka, gaba daya adadin ya kai 1,100,283 a fadin duniya, inda adadin wadanda suka rasa ransu a sanadin cutar ya kai 58,929.

Alkaluman sun kuma nuna cewa, Amurka ta kasance kasar da cutar ta fi kamari, inda mutanen da aka tabbatar sun kamu suka kai 277,965, wadanda suka mutu sakamakon cutar kuma sun kai 7,157. Kana Italiya ta kasance kasar da ta fi yawan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon cutar, inda adadinsu ya kai 14,681, kuma adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 119,827. Ban da wadannan kasashe biyu, 'yan kasar Spaniya wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar sun kai 119,199, a cikinsu, wadanda suka mutu sun kai 11,198.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China