Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministocin kudin kasashen Afrika sun bukaci samar da dala biliyan 100 domin tunkarar annobar COVID-19
2020-04-02 11:18:18        cri

Ministocin kudin kasashen Afrika, sun bukaci a gaggauta samar da dala biliyan 100 domin tunkarar barkewar cutar COVID-19 a nahiyar.

Sanarwar da hukumar kula da tattalin arzikin Afrika ta MDD (ECA) ta fitar, ta ce wannnan batu ya zo ne a Talata, yayin taron bidiyo na 2 da ministocin suka yi, dangane da tunkarar karuwar bazuwar cutar a nahiyar.

Da suke yabawa dabarun da gwamnatoci suka dauka, ministocin sun ce tattalin arzikin nahiyar na tafiyar hawainiya, wanda ka iya daukar shekaru 3 kafin ya farfado.

Sun kuma jaddada muhimmancin daukar dukkan mai yuwuwa wajen takaita yaduwar cutar cikin gajeren lokaci, amma sun amince cewa, jan aiki ne.

Ministocin da galibi suka bayyana a taron sanye da marufin hanci da baki, sun kuma amince cewa, dole ne a ci gaba da bada muhimmanci ga harkar kiwon lafiya da ayyukan jin kai, domin a ci gaba da kara wayar da kan jama'a da yin gwaje-gwaje da kuma nisanta mu'amalar jama'a. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China