Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
COVID-19 ta hallaka mutane 72 a Afirka cikin sama da mutum 2,746 da cutar ta harba
2020-03-26 20:49:28        cri
Cibiyar dakile yaduwar cututtuka da kandagarkinsu ta nahiyar Afirka ko CDC a takaice, ta ce ya zuwa Alhamis din nan, adadin mutanen da cutar numfashi ta COVID-19 ta hallaka a nahiyar Afirka sun kai mutum 72, yayin da cutar ta harbi mutane sama da 2,746 a kasashen nahiyar 46.

Cibiyar ta CDC, wadda ta bayyana hakan cikin alkaluman da take fitarwa, ta ce kasashen Afirka 16, sun tabbatar da rasuwar mutane 72 bayan fama da cutar ta COVID-19.

Kasashen da annobar cutar ta fi kamari dai sun hada da Afirka ta Kudu mai mutane 709, da Masar mai mutum 456, da Algeria mai 302, sai kuma kasar Morocco mai mutane 225.

Cikin jimillar wadanda cutar ta harba a nahiyar Afirka, cibiyar ta CDC ta ce akwai mutane 210, daga kasashe 14 da tuni suka warke bayan samun kulawar jami'an lafiya.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China