Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ghana za ta fara gwajin cutar COVID-19 na gama gari a kasar
2020-03-31 10:33:18        cri

Jami'an kiwon lafiyar kasar Ghana za su fara aikin gwajin cutar numfashi ta COVID-19 a dukkan yankunan kasar, wani babban jami'in fadar shugaban kasar ne ya tabbatar da hakan.

Tawagar jami'an binciken lafiyar kasar Ghana za su ziyarci dukkan gidajen jama'a a yankunan da aka killace a kokarin gwamnati na dakile bazuwar cutar a fadin kasar.

Nsiah Asare, mashawarci na musamman ga shugaban kasar a fannin kiwon lafiya ya ce, duk wani gidan da aka samu mutumin da sakamakon gwajinsa ya nuna yana dauke da cutar za'a killace su baki daya.

Jami'in ya bukaci al'umma da su baiwa tawagar jami'an lafiyar cikakken hadin kai a lokacin da suka ziyarci gidajen jama'ar don gudanar da aikin.

Ya ce ba za su zuba ido har sai an samu alamaun kamuwa cutar ba tare da yin gwajin ba. A cewarsa za su ci gaba da yin gwaje-gwajen ba tare da yin jinkiri ba, a cewar tsohon babban daraktan hukumar lafiyar kasar Ghana.

Ya zuwa ranar Litinin, Ghana tana da mutane 152 da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19, yayin da mutane biyu suka warke, sai mutane biyar da suka mutu a sanadiyyar cutar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China