Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta gama aikin gwajin sabon kumbo dake daukar dan Adam
2020-03-26 10:39:28        cri

Rahotanni daga kamfanin kimiyya da fasahar sararin samaniya na kasar Sin na cewa, Sin ta kammala aikin gwajin sabon kumbo dake daukar dan Adam a filin harbar tauraron dan Adam gami da roka dake garin Wenchang na lardin Hainan a kwanakin baya, daga baya za a yi gwajin harbar shi ta hanyar amfani da roka samfurin Changzheng-5B.

An tsara sabon kumbo ne ta yadda zai dace da tashar binciken sararin samaniya ta Sin da ayyukan binciken sararin samaniya ta kumbo dake daukar dan Adam. Idan aka kwatanta shi da kumbon Shenzhou, sabon kumbon ya fi shi girma, kuma zai dauki mutane da kaya, kana za a iya sake yin amfani da shi. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China