Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mayakan Boko Haram sun halaka sojojin kasar Chadi 92
2020-03-25 09:17:55        cri
Rahotanni daga kasar Chadi na cewa, sojojin kasar 92 ne suka gamu da ajalinsu, kana wasu 47 kuma suka jikkata, a wani hari da mayakan Boko Haram suka kaddamar a ranar Litinin a garin Boma na lardin Lac dake yankin arewacin kasar.

Shugaban kasar Idriss Deby Itno, shi ne ya sanar da haka a ranar Talatar da ta gabata, ya ce lamarin ya faru ne lokacin da sojojin ke kan hanyarsu ta zuwa N'Djamena don ba da kulawar gaggawa a garin na Boma.

Shugaban ya yi alkawarin cewa, sojoji za su sake bitar duk kan shirye-shiryen da suka tsara don kaucewa abin da ya faru a garin na Boma.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China