Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wasu manyan mutanen Afirka sun yi kira da a hada kai domin fuskantar cutar COVID-19
2020-03-24 14:00:17        cri

Wasu 'yan siyasa na kasar Amurka sun kira cutar numfashi ta COVID-19 "cutar Sin", dangane da wannan batu, wasu manyan mutanen kasashen Afirka da dama sun bayyana cewa, kasar Sin ta yi nasarar dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 bisa managartan matakan da ta dauka a kan lokaci. A halin yanzu, aiki mafi muhimmanci dake gabanmu shi ne yin hadin gwiwa wajen hana yaduwar cutar, a maimakon yin zargi ko kuma bata sunan wata kasa.

Ministar harkokin kiwon lafiyar kasar Habasha Lia Tadesse ta bayyana cewa, cutar numfashi ta COVID-19 ta kasance babban kalubale ga dukkanin kasashen duniya. Ta ce, "Wannan cuta ta haifar da hadari ga dukkanin bil Adama, ko mece ce kabilarku, al'adunku, launin fatarku da kuma addinanku. Don haka, bai kamata mu danganta ta da wasu mutane na wani yanki, ko launin fata ko kuma kabilu da sauransu ba. Ya kamata gamayyar kasa da kasa su hada kansu domin fuskantar annobar, a maimakon danganta wannan cuta da wata kasa ko wata kabila. Dole ne mu hada gwiwa wajen yaki da cutar, ta yadda za mu yi nasarar wannan yaki."

A nasa bangare, shugaban cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasashen Afirka John Nkengasong ya bayyana cewa, muna bukatar kasashen duniya su hada kai domin yaki da cutar numfashi ta COVID-19, bai kamata mu bata suna ko nuna bambanci kan wata kasa ba. Yana mai cewa, "A ganina, wannan yaki ne na kasashen duniya baki daya, kamata ya yi kasashen duniya su hada kai, a maimakon bata sunan kasashen Asiya ko kuma nuna bambanci kan wadanda suka taba kamu da kuma yada wannan cuta. Abokin gaban mu ita ce cutar numfashi ta COVID-19, ba Afirka ba, ba kasashen Turai ko Amurka ba. Ya kamata mu mai da hankali matuka kan babban abokin gabanmu wato cutar numfashi ta COVID-19."

Shi kuwa, jakadan kasar Djibouti dake kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta AU Mohammed Idris Farah ya nuna yabo matuka kan matakan da kasar Sin ta dauka wajen yaki da cutar, ya ce, ya dace kasashen Afirka su koyi fasahohin da kasar Sin ta yi amfani da su wajen yaki da wannan cuta. "Ya kamata kasashen Afirka su koyi fasahohin da kasar Sin ta yi amfani da su wajen yaki da annobar, sabo da kasar Sin ta yi nasarar dakile yaduwar cutar bisa managartan matakan da ta dauka a kan lokaci, a don haka ya kamata su ma kasashen Afirka su dauki irin wadannan matakai. Kasashen Afirka ba su da isassun kudade na yin yaki na dogon lokaci, a don haka, ya dace su yi hadin gwiwa da abokansu kamar kasar Sin da sauransu wajen yaki da annobar."

Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na kasar Habasha shi ne kamfanin jiragen sama mafi girma a nahiyar Afirka, a ranar 22 ga wata, jiragen dakon kaya na kamfanin suka yi jigilar kayayyakin kiwon lafiya da Sin ta samar zuwa birnin Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha. Babban jami'in kamfaninTewolde Gebremariam ya bayyana cewa, "Hakika, abin bakin ciki ne, yadda wannan cuta take yaduwa cikin sauri a kasashen Afirka, Amurka, da ma kasashen Turai, wato yadda take yaduwa a sassan fadin duniya. A don haka, ya kamata mu yi kokarin hada kai domin kare kanmu. In ba haka ba, mu ci gaba da zargin wani ko wata, ta yadda za mu kasa mai da hankali kan wannan cuta yadda ya kamata. Firaministan kasarmu da Jack Ma sun tsara wani shirin samar da kayayyaki, shi ya sa muka fara hada kai don ganin kwalliya ta biya kudin sabulu. Yanzu, muna jigilar kayayyaki, domin tabbatar da kiyaye lafiyar al'ummominmu yadda ya kamata. Amma kokarin bata sunan wani ko wata ba zai haifar da wani da mai ido ba." (Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China