Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Likitancin gargajiyar kasar Sin na tallafawa kasa da kasa wajen tinkarar COVID-19
2020-03-20 15:00:01        cri

 

A ranar 11 ga wata, an kira wani taron ta kafar bidiyo a tsakanin kwararru a fannin likitancin gargajiyar kasar Sin da suka fito daga Beijing, Zhengzhou, Hongkong na kasar Sin, da Rome na Italiya, Toronto na Canada da kuma Singapore, inda kungiyar kwararru ta kamfanin Tongrentang na kasar Sin, ta samar da takardar likitanci ta sayen magani irin na kandagarki da shawo kan cutar COVID-19, bisa fasahohin da aka samu wajen yaki da annobar.

Mataimakiyar babban manajan kamfanin Tongrentang madam Ding Yongling ta gayawa wakilinmu cewa, "Ta hanyar magunguna, kwararru, da manyan bayanai, da kuma kimiyya da fasahar zamani, mun tabbatar da amfanin shirye-shiryen kandagarki da shawo kan cutar COVID-19, bisa yanayin musamman da kasashe daban daban suke ciki, mun kuma samar da wadannan shirye-shiryen da muka tsara bisa likitancin gargajiyar kasar Sin ga jama'ar kasa da kasa, ta hanyar dandalin yanar gizo guda 149 namu dake bazuwa a kasashe da yankuna 28."

 

 

A yayin da ake tinkarar annobar, hukumomin likitancin gargajiya na duk kasar Sin sun aika da likitoci, da nas nas kusan 3200 zuwa lardin Hubei, inda cutar ta yi kamari. Ya zuwa ranar 13 ga wata, adadin amfani da maganin gargajiyar Sin ya kai kashi 91 cikin 100 a lardin. Sakamakon nazari ya shaida cewa, idan aka kwatanta da amfani da maganin gargajiya ko maganin zamani kadai, amfani da maganin iri biyu baki daya, yana taimakawa wajen kyautata alamun kamuwa da cuta cikin sauri, ciki har da zazzabi, tari, rashin karfi da dai sauransu, kana da kara yawan wadanda suka warke daga cuta, da rage yawan mutanen da suka mutu sakamakon cuta.

Cutar numfashi ta COVID-19, wata irin annoba ce. Kasar Sin na da dogon tarihi mai tsawon dubu-duban shekaru wajen yaki da annoba. Sakamkon amfanin likitancin gargajiyar kasar Sin, ba a taba ganin bullar babbar annoba da ta haifar da rasuwar dubban miliyoyin mutane a tarihin kasar ba.

Ga misalin, a yayin da ake tinkarar cutar SARS da ta bulla a shekarar 2003, birnin Guangzhou na kasar Sin ya dauki hanyar likitancin gargajiyar kasar Sin don shawo kan cutar, asibiti mallakar jami'ar koyar da likitancin gargajiyar kasar Sin ta birnin, ya karbi mutanen da suka kamu da cutar guda 58, dukkansu ba su rasa rayukansu, kuma ba a ci gaba da yaduwar cuta ba. A nasa bangaren, asibitin Xiaotangshan dake birnin Beijing tun bayan ya soma amfani da likitancin gargajiya, wadanda suka kamu da cutar su ma sun ragu sosai.

Yadda sakamakon jinyar yake, shi ne ma'auni na kimanta fifikon likitancin gargajiyar kasar Sin. Shi ne kuma ginshiki da dama na likitancin gargajiyar kasar Sin wajen fita daga kasar, don shiga ayyukan kandagarki da shawo kan annoba.

 

Shugaban jami'ar koyar da likitancin gargajiyar kasar Sin ta Tianjin, mista Zhang Boli ya bayyana cewa, kungiyar kwararru ta kai magungunan gargajiyar da suka hada da Lianhuaqingwen, da Jinhuaqinggan a wasu kasashe, ciki har da Italiya, Iraki da dai sauransu, ya zuwa yanzu kuma an gano cewa, irin wadannan magunguna suna da amfani sosai wajen shawo kan cutar numfashi ta COVID-19 marasa tsanani da ta kullum.

 

 

Kwanan baya, hukumomin lafiyar kasar Iran sun bayyana fatansu na ganin kasar Sin ta iya samar musu fasahohi da shirye-shiryen jinya. Kwararru na kasar Sin ma sun riga sun ba da shawar cewa, game da wadanda suka yi mua'amala sosai da masu kamuwa da cutar, ta yadda za a yi amfani da maganin Huoxiangzhengqidiwan, ga wadanda suka kamu da cutar, da wadanda ake zaton sun kamu da cutar, yadda za su sha maganin Lianhuaqingwen da Jinhuaqinggan.

Ya zuwa yanzu, likitancin gargajiyar kasar Sin na yaduwa a kasashe da yankuna 183. A yayin da ake tinkarar annoba, an kara fahimta da amincewa da fifiko da amfaninsa.

Bisa karuwar yawan mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 a kasar Burtaniya, yawan magungunan gargajiyar kasar Sin na yaki da cutar da aka sayar a birnin London ya karu har ninki 10. A waje guda kuma, likitoci na likitancin gargajiyar kasar Sin sama da 50 da suka fito daga birane 20 da wani abu na kasar Burtaniya, sun tayar da wani aikin sa kai, inda ta dandalin sada zumunci suka samar da bayyanai game da yadda ake kandagarki da shawo kan cutar, ta hanyar amfani da likitancin gargajiyar.

A yayin da ake tinkarar annobar a duk duniya, kasar Sin tana son more fasahohin da ta samu da shirye-shiryen jinya da ta tsara, don sanya kasashe mafi yawa su fahimci da amfani da likitancin gargajiyar kasar. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China