Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan wadanda suka kamu da COVID-19 a Najeriya ya karu zuwa 30
2020-03-23 09:11:26        cri

Hukumomin lafiya a Najeriya sun bayyana cewa, a zuwa jiya Lahadi an tabbatar da yawan mutane 30 da suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a kasar, inda a jiya Lahadi, aka kara samun sabbin mutane 8 da suka kamu da cutar.

Da take karin haske cikin wata sanarwa da ta rabawa manema labarai, hukumar kare yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta bayyana cewa, an kara samun mutum guda a Abuja, babban birnin kasar cikin sabbin mutane takwas din da aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar.

Hukumar ta ce, a jiya Lahadi, an kara samun mutane 6 da suka kamu da COVID-19 a Lagos, cibiyar kasuwancin kasar, inda ta tabbatar da adadin mutane 22 da suka kamu da cutar a jihar.

Ya zuwa yanzu dai, gwamnatin Najeriya ta dauki matakan hana yaduwar cutar, wadanda suka hada da, kara rufe iyakokin shiga kasar da haramta shiga da fita na dukkan jiragen sama a cikin kasar. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China