Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zhang Weili 'yar wasan Sin ta kare kanbin ta na UFC ta kuma sadaukar da shi ga yaki da COVID-19
2020-03-12 20:25:03        cri


'Yar wasan Sin daya tilo, kuma ta farko da ta taba lashe kambin dambe na duniya ajin matsakaicin nauyi a gasar UFC Zhang Weili, ta doke abokiyar karawar ta Joanna Jedrzejczyk ta Poland, a dambatawar da suka yi a birnin Las Vegas a gasar UFC ta 248, a Asabar din karshen makon jiya.

An dai kai ruwa rana kwarai kafin Zhang ta cimma nasarar lashe gasar, inda aka ba ta kambin gasar, bayan amincewar alkalan wasan. Zhang ta samu amincewar alkalan da maki 48 sama da 47 da abokiyar karawar ta ta samu.

Zhang, 'yar asalin lardin Hebei, ta samu karbuwa sosai daga magoya baya, da masu sha'awar damben na UFC, to sai dai fa yayin da suke dambatawa, kusan abu ne mai wuya a iya gane wacce ke sahun gaba, ganin yadda suke matukar bawa hammata iska. Sun yi ta dauki ba dadi da juna, kana ko waccen su ta sha naushi masu tarin yawa yayin da suke tsaka sa gumurzu.

Jedrzejczyk, wadda a baya ke rike da kambin gasar Muay Thai, ta fara damben na wannan lokaci da sa'a, inda ta rika naushin abokiyar karawar ta ta hanyar naushi da hannu da kafa ta ko wace dama da ta samu.

To sai dai kuma, duk da kokarin Jedrzejczyk na cin gajiyar tsayi da take da shi kan abokiyar karawar ta, Zhang ta nuna mata ba a nan take ba.

Zhang ta dage kwarai a zagayen farko na gasar, inda ta rika maida martani da naushi iya karfin ta, duk da matsi da ta sha daga Jedrzejczyk a duk tsawon fafatawar su zangon farko.

A zagaye na biyu ma, Jedrzejczyk ta ci gaba da matsa kaimi, yayin da ita ma Zhang ba ta yi kasa a gwiwa ba, wajen maida naushi ta ko wace kofa ta samu. A bangaren zagaye na 2 na gasar, Zhang ta kara harinta kan Jedrzejczyk, wanda hakan ya rage matsin da ta fuskanta da farko. Bugu dakari, Zhang ta fara amfani da dabarun naushi mafiya tasiri da ya hana abokiyar karawar ta sakat.

Yayin da take kara matsa kaimi wajen kai naushi, Zhang ta fara nuna alamun gajiya, amma duk da haka jarumar ta Sin ta ki dakatawa, a zagaye na 3 da na 4, alamu sun nuna cewa Zhang ta gaji sama da abokiyar karawar ta. Duk da haka, yayin da ta rage kai naushi masu yawa, Zhang ta ci gaba da nuna kwarewa da dabarun tabbatar da ta kai karshen wasan cikin nasara, sama da dabarun da Jedrzejczyk ke amfani da su a wasan.

A zagayen karshe na gasar, Zhang ta samu nasara a karo na 2, inda ta farfado da kuzarin ta. Zhang, wadda 'yan mintuna kadan ta nuna ta gaji, ta yunkuro da kwazon ta na musamman. Jedrzejczyk kuwa, wadda dukkanin fuskarta ke kumbure, ta ci gaba da karbar naushi masu nauyi daga Zhang, wanda ya kai ga hancin ta ya sauya kama. A karshen damben, Zhang da Jedrzejczyk sun yiwa juna naushi masu zafin gaske, kana aka bar alkalai da yanke hukunci.

Bayan kammala wasan, Zhang cike da jimami, ta gabatar da sakon ta na jaje ga yakin da Sin ke yi da cutar COVID-19, tana mai jinjinawa kwazon masu sha'awar wasanta, bisa goyon baya da suka nuna mata a wannan lokaci.

Sakamakon bullar cutar numfashi ta COVID-19, Zhang Weili ta tashi zuwa kasar Thailand inda ta yi makwanni 2, kafin ta tashi zuwa Amurka domin damben. Ta ce "Ina fatan kasa ta za ta shawo kan wannan cuta cikin sauri, duk da cewa yanzu annobar ta wuce batun kasar Sin kadai. Ta ce annobar ta shafi dukkanin bil Adama ne. Ina fatan kowa da kowa za mu yi aiki tare domin kawo karshen wannan annoba".

A watan Janairu, Joanna ta wallafa hoton ta a kafar dandalin sada zumunta sanye da murfin hanci da baki. Yayin taron ganawa da manema labarai gabanin damben, ta rika kalubalantar Zhang Weili tana ce mata bola. To sai dai Zhang Weili ta maida martani da cewa: "Abokiyar karawar ta tana da fadin rai, da rashin ban sha'awa. Tana yiwa wasu dariya a halin da suke ciki na damuwa. Al'adar mu ta Sinawa na tattare da taimakawa mutane dake cikin mawuyacin hali. Wannan ya fusata ni, idan kina tunanin suka ta zai sa ki karin karfi, ki yi hakan, amma hakan ba abun wasa ba ne. "

Zhang Weili 'yar shekaru 31, iyayen ta masu aikin ma'adanai ne, ta kuma shiga makarantar koyon wasanni da dabarun kare kai ko "Martial Art" tun tana da shekaru 12 a duniya. Ta taba lashe lambar yabo ta gasar "Sanda championship" da aka gudanar a lardin Hebei, daga bisani kuma ta koma kwalejin koyon fada ta MMA.

Sabanin yara da dama da iyayen su ke tura su irin wannan makaranta, Zhang Weili ita ta zabi wannan makaranta. Kasancewar ta mai kiriniya tun tana karama, kamar yara maza a fagen wasanni, tana kuma da kwarewa wajen shiga wasanni daban daban. Ta yi wasanni daban daban na tsere a lokacin tana firamare, kuma yanayin jikin ta ya dara na wasu yaran maza ma. A wannan lokaci, a gabar da fina finan "Martial Art" na yankunan Hong Kong da Taiwan ke tashe, Zhang Weili mai shekaru 8 da haihuwa, a lokacin ta rika sha'awar taurarin da ke fitowa a fina finai da sauran wasanni masu hadari a kafar Talabijin, ta kuma rika burin zama mai karfin hali kamar su, kana ta roki mahaifiyar ta ta tura ta makarantar koyon fada. Zhang Weili ta shiga makarantar tana da shekaru 12, kuma ba tare da bata lokaci ba ta fara lashe lambobin yabo. Tana da shekaru 14 kuma, ta lashe gasar "Sanda championship" ta lardin Hebei.

Tana kuma tana 'yar shekaru 17, sakamakon raunuka da matsi daga iyayen ta, Zhang Weili ta amince ta yi ritaya, ta kauracewa karbar kudade ko tallafin iyayen ta, ta shiga harkokin zamantakewar al'umma ita kaidai. Ta yi aikin sabis, da gadi, malamar makarantar yara kanana, mai bada kariya ga wasu mutane, da mai ba da horo a dakunan motsa jiki.

A shekarar 2012, Zhang ta gamsar da mahaifanta game da burin ta na fara samun horo na dambe a ajin kwararru. Ta fara da koyon salon damben kasar Brazil na jujitsu, daga nan ta koma koyon salon fada na MMA. A matsayin kwararri a fannin wasan daben MMA. Wasa daya Zhang Weili ta taba yin rashin nasara, inda a lokacin ta yi rashin nasara da maki 20 da 1. Shi ne rashin nasara daya tilo da ta yi a dukkanin sana'ar ta ta dambe.

A watan Agustar shekarar 2019, Zhang Weili ta cimma nasarar doke 'yar damben kasar Brazil Jessica Andrade cikin dakiku 42, a gasar UFC da ta gudana a birnin Shenzhen, inda ta zama 'yar dambe ta farko a kasar Sin da ta lashe gasar UFC.

A daya bangaren kuma, dan wasan damben Sin a gasar UFC ta 248, Li Jingliang wanda ke rike da kambin gasar Shenzhen da ta gudana watanni 6 da suka gabata, kashi ya sha a hannun Neil Magny na Amurka, bayan da daukacin alkalan gasar suka ce ba'amurken ne ya yi nasara a gasar.

A wani wasan na daban, shi ma dan wasan damben Najeriya mazaunin New Zealand Adesanya, nasara ya samu kan Yoel Romero daga Cuba, a dambatawar da ta yi matukar daukar hankali 'yan kallo.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China