Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Afrika ba zata karbi bakuncin gasar wasannin motsa jiki na kasa da kasa a shiyyar ba
2019-12-13 15:11:53        cri

Nahiyar Afrika ba zata karbi bakuncin sabbin nau'ikan wasannin motsa jiki na kasa da kasa da aka kaddamar a shiyyar ba, wasannin wasu jerin wasannin kwararru ne wadanda bai shafi wasannin Diamond League ba.

Ana sa ran sabbin wasannin zasu cike gibin da aka samar bayan wasannin Diamond League a lokuta daban daban, wadanda suka kunshi wasannin tsere na dogo da matsakaicin zango, wanda a tarihi galibin 'yan wasannin Afrika ne ke mamaye wasannin.

Wasannin sun kunshi karawar da za'a yi a tsakanin 'yan wasanni daga sassa daban daban na duniya za'a rarraba wasannin zuwa bangarori uku, wato na zinare, da azurfa, da kuma tagulla wanda za'a tabbatar da matsayinsa ta hanyar ingancin gasar da kuma bayar da kyautar kudade.

Shugabannin wasannin motsa jiki na kasa da kasa suna zuba jari a matakan zinare da nufin kara yawan ingancin wasannin don samar da damammaki ga kwararrun 'yan wasa, inji Sebastian Coe, shugaban wasannin motsa jiki na kasa da kasa.

A shekarar 2020, shekarar farko da za'a yi ran gadin, kimanin birane 10 ne zasu karbi bakuncin gasannin matakin zinare, wanda aka ware kudade da adadinsa ya tasamma dalar Amurka miliyan biyu.

Za'a fara zagayen wasannin ne a watan Mayu a Tokyo, a filin wasan da zai karbi bakuncin gasar wasannin motsa jiki ta Olympic 2020 bayan watanni uku. Daga bisani kasar Sin zata karbi bakuncin zagaye na biyu na wasannin a watan Mayu a Nanjing.

Sauran wuraren da za'a gudanar da nau'ikan wasannin sun hada da Golden Spike a Ostrava, da jamhuriyar Czech, da Hanzekovic Memorial dake Zagreb babban birnin kasar Croatia da kuma Racers Grand Prix dake Kingston na kasar Jamaica.

Kungiyoyin yankunan ne zasu dauki nauyin shirya wasannin Azurfa da Tagulla, wanda zai kunshi wasannin kimanin 100 daga dukkan sassan duniya.

Coe yace, "Mun fara taron gangamin rangadin shirya wasanni masu inganci a fadin duniya da sabbin wasannin motsa jiki na shiyyoyi, wanda zai samar da Karin damammaki ga masu shiga wasannin motsa jikin don taka rawarsu a dukkan fannoni, inda zasu samu kyautukan kudade da samun lambobin yabo masu daraja na kasa da kasa kuma don su samu damar shahara a duniya a fannonin da suka kware".

"Tsakanin wasannin kwararru na Diamond League da wasannin motsa jiki na shiyya, za'a bada kulawa ga dukkan fannoni kuma wasu nau'ikan sabbin wasannin motsa jiki zasu samu damar shiga manyan gasanni mafiya daraja. Wasannin da ba'a samu damar shigar dasu a gasar karshe ta Diamond League ba, zasu kasance wasannin dake sahun gaba a shiyyo a shekara mai zuwa."

Za'a bayar da kyautar kudade da suka kai dalar Amurka 200,000 ga kowane wasannin zinare , da kuma bayar da maki mafi daraja a duniya.

A muhimman wasanni na kakar wasannin 2020 da suka hada da wasan gudun ketare shingen ruwa na mitoci 200 da 3,000, da tsallen badake, da jifan mara, da jifan dalma, ga rukunin 'yan wasa maza da mata dukkansu za'a basu maki daidai da matsayin wasannin Diamond League.

Za'a bayar da katin shiga gasar wasannin motsa jiki ta duniya ta kwararru ta 2021 da za'a yi a Oregon ga 'yan wasan da suka fi nuna kwazo a fannoni daban daban.

A kowane zagayen wasa an kebe kimanin dala 20,000 wato dala 6,000 ga wanda ya lashe gasar da kuma dala 10,000 a kowane zagayen gasar sannan duk wanda ya lashe gasar zai samu kyautar dala 3,000.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China