Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Motsa jiki ya fi muhimmanci wajen kiyaye lafiyar jikin dan Adam
2020-03-02 09:28:22        criA halin yanzu, batu mafi jan hankalin jama'ar kasar Sin har ma jama'ar duniya baki daya shi ne abkuwar cutar numfashi ta COVID-19 a nan kasar Sin. Cutar numfashi ta COVID-19 ta barke ne a birnin Wuhan dake lardin Hubei na kasar Sin, inda ta fara bazuwa a kasar. Ya zuwa yanzu, adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a lardin Hubei da cutar ta fi kamari ya zarce 63000, kana adadinsu a dukkan kasar Sin ya zarce 76000. Gwamnatin kasar Sin ta dauki matakan magancewa da yaki da cutar cikin sauri, hukumomin wurare daban daban na kasar Sin sun yi kokarin dakile yaduwar cutar. Domin ana iya baza wannan cuta a tsakanin 'yan Adam, ya sa gwamnatin kasar Sin ta yi kira ga dukkan jama'ar kasar da su zauna a cikin gida, da kauracewa taruwar jama'a, da kuma sanya abin rufe baki da hanci a koda yaushe a waje da sauransu don kare kai daga kamuwa da cutar.

A halin yanzu, lardin Hubei musamman birnin Wuhan ya fi jan hankalin jama'a, domin yawancin mutanen da suka kamu da cutar sun fito ne daga wannan wuri. Don haka, tun daga ranar 23 ga watan Janairu, aka dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa, da na sama, da motoci a birnin Wuhan, an kuma dauki matakai daban daban don hana taruwar mutane. Mazaunan birnin Wuhan sun dakatar da fita waje, inda suke zaune a gida.

Xiao Fan, wani mazaunin birnin Wuhan, bayan abkuwar cutar, ya dakatar da fita waje, sai dai idan batu ne na gaggawa. Idan kuma zai fita waje, ya kan sanya abin rufe baki da hanci, ya tube rigarsa ya ajiye ta a wajen taga, da kashe kwayoyin cuta kan riga, da kuma tsabtace hannu sau da dama. Ya ce, gwamnatin birninsa ta dauki matakai masu amfani, ya kamata shi da sauran mazaunan birnin Wuhan su yi imani da gwamnati, su daina fita waje, da kula da lafiyarsu, don hana kawo cikas ga aikin kawar da cutar domin. Malam Xiao ya bayyana cewa, a matsayin dan birnin Wuhan, birni mafi fama da cutar, abin mafi muhimmanci shi ne kada a biyewa jita-jita, da yin imani da gwmanatin kasar.

Ya ce,"A ganina, abin mafi muhimmanci shi ne kada a biyewa jita-jita, kuma kada a yada jita-jita, mun ji labarai daga bangaren gwamnati, da kuma tabbatar da lafiyarmu ta hanyar kimiyya da fasaha."
Xiao Fan ya ce, koda yake ba ya motsa jiki, amma ya san motsa jiki zai taimakawa mutane wajen tabbatar da lafiyar da tinkarar cuta. Ya ce,

"Yayin da nake zaune a cikin gida a wannan lokaci, na kan yi rubuce-rubuce da alkalamin gashi don samun nutsuwa, kana na yi amfani da manhajar wayar salula don motsa jiki a gida. Motsa jiki zai inganta karfi da lafiyar jikin mutane."
Ban da birnin Wuhan, sauran wuraren lardin Hubei su ma sun fi fuskantar cutar numfashi ta COVID-19. Babu shakka, dukkansu sun dauki matakan kariya da yaki da cutar kamar birnin Wuhan. Pan Xiang, wani mazaunin garin Badong dake lardin Hubei, bayan abkuwar cutar, an hana ziyartar iyalai da abokai a lokacin hutun bikin bazara, kana an rufe hanyoyin motoci dake kewayen garinsa, don hana yaduwar cutar a garin. Kamar yadda dukkan Sinawa ke yi a wannan lokaci, ya kan sanya abin rufe baki da hanci yayin da yake a waje. Game da motsa jiki kuwa, ya ce a halin yanzu, lafiyar jiki ta fi komai, ya kamata kowa ya rika motsa jiki a wannan lokaci. Ya ce,

"Na kan motsa jiki a cikin gida kamar su yin tsalle-tsalle, da kwanciya ruf da ciki da sauransu don kula da lafiyar jiki da lafiyar zuciya da huhu. Ina fatan za a kawo karshen cutar numfashi ta COVID-19 cikin sauri."

Kong Lingxue, wata malama ce mai koyar da Turancin Ingilishi a makarantar firamare dake yankin Enshi na lardin Hubei, ta bayyana cewa, an riga an dakatar da dukkan darussa a makarantar firamaren da take komawa, yara na yin karatu a gida ta yanar gizo. Game da matakan da ake dauka a yankinta, ta ce jama'ar dake yankin suna zaune a cikin gida, da yin bincike kan zafin jikinsu a kowace rana. Kana likitoci su kan je gidajensu don duba lafiyarsu. Ita ma ta yi tsammani cewa, motsa jiki ya fi muhimmanci wajen kiyaye lafiyar jikin mutane. Ta bayyana cewa,"Babu shakka motsa jiki ya fi muhimmanci a lokacin tinkarar cutar numfashi ta COVID-19, na kan yi tsalle da igiya, da yin tafiya a cikin gida. A ganina, motsa jiki zai taimaka wajen kula da lafiyar jiki, kana zai kwantar da hankali a wannan lokaci. Ban da motsa jiki, na kan yin karatu a lokacin, wannan lokaci ya kawo mana wata muhimmiyar dama wajen kara yin karatu don inganta aikinmu."

Kong Lingxue tana fatan za a kawo karshen cutar cikin sauri, da mayar da zaman rayuwar jama'a yadda ya kamata, kana tana fatan hukumomin da abin ya shafa za su koyi fasahohi daga wannan batu, don tinkarar irin wannan yanayi a nan gaba. A ganinta, hukumomin garinsu sun dauki matakan kariya da yaki da cutar yadda ya kamata, duk wanda ya shiga gari daga wasu wurare ya kamata ya zauna a cikin gida har na tsawon kwanaki 14, ba tare da fita waje ko kadan ba, don magance yaduwar cutar.

Dan uwanta mai suna Kong Lingshuang ya je birnin Wuhan kafin ya koma garinsu wato yankin Enshi na lardin Hubei, don haka ma'aikatan hukumomin garinsu su kan buga masa waya don tambayarsa ko yana jin zafin jiki ko a'a, kana su kan je gidansa don duba lafiyarsa a wasu lokuta. Kong Lingshuang ya yi tsammani cewa, matakan da hukumomin garinsa suka dauka suna da amfani, an dakatar da zirga-zirgar jama'a da motoci, da hana taron jama'a, hakan zai iya magance yaduwar cutar. Kana hukumomin su kan koyar da jama'a fasahohin kare kansu, kamar sanya abin rufe baki da hanci, da tsabtar gida, da wanke hannu sau da dama da sauransu. Kazalika kuma lokacin da jama'a ke cikin gida, ya kamata su motsa jiki don kula da lafiyarsu. Koda yake ba a iya fita waje, kuma ba a iya zumunci da iyalai da abokai, akwai wasu abubuwan da ake iya yi a cikin gida. Ya ce,"Kula da lafiyar jiki ya fi muhimmanci a kowane lokaci. A gida, na kan motsa jiki mai sauki, kamar su yin kwanciya ruf da ciki, da yin tafiya cikin gida. Idan akwai dama, na yi wasan kwallon badminton. Ina motsa jiki don inganta lafiyar jikina, da kuma sassauta damuwa a wannan lokaci, wato ya na taimakawa mini samun nutsuwa a zuciya."

Kong Lingshuang ya kara da cewa, koda yake wannan cuta ta abku ba zato ba tsammani, sannan ya yi tsananin a lardinsu, amma matakan da hukumomin lardin da kuma garinsu suka dauka sun taimakawa jama'a da magance kamuwa da cutar da yaki da ita. Yana fatan za a cimma nasarar yaki da cutar cikin hanzari, kuma jama'a su mayar da zaman rayuwarsu yadda ya kamata. Kana yana fatan masu aikin jinya da masu kulawa da wadanda suka kamu da cutar za su tabbatar da kula da lafiyarsu, da kare kansu. Ya kuma gode musu domin sun bada babbar gudummawa wajen yaki da cutar.

Lardin Hubei musamman birnin Wuhan ya fi fuskantar matakan yaki da cutar numfashi ta COVID-19, gwamnati da hukumomin wurin sun yi namijin kokari wajen daukar matakan kariya da yaki da cutar. Jama'ar dake zaune a yankin sun yi imani da su, da bin matakan da aka dauka. Sun zauna a cikin gida, ba tare da fita waje ba. Idan za su fita waje, su kan sanya abin rufe baki da hanci, da wanke hannu sau da dama, da kuma tsabtace riga da takalma bayan sun koma gida. Kamar yadda dan birnin Wuhan Xiao Fan ya fada, babu bukatar jin tsoron cutar, ya kamata su kare kansu, da tabbatar da lafiyar jikinsu, kada a kara nauyin aiki kan masu aikin jinya da masu kulawa, sakamakon kamuwa da cutar. Jita-jita ta fi tsanani, bai kamata a yarda da su ba, bin matakan gwamnati da yin imani da gwamnati za su taimaka wajen cimma nasarar yaki da cutar. Xiao Fan ya ce,"Bayan abkuwar cutar, a kan ji jita-jita iri daban daban, watakila ana fitar da wasu jita-jita domin a kara jin tsoron wannan sabuwar cuta, amma wasu suna da mugun nufi. Mu muna rayuwa a birnin Wuhan, wanda birni ne mafi fuskantar cutar, mun san hakihakin yanayin da ake ciki. Abin mafi muhimmanci shi ne mu tantance gaskiya da jita-jita. A halin yanzu, ya kamata mu kare kanmu, mu motsa jiki domin kula da lafiya, da yaki da cutar."

Koda yake cutar numfashi ta COVID-19 ta kawo babbar illa ga lafiyar jikin jama'ar Sin da kuma zaman rayuwarsu, amma jama'ar Sin sun hada kai, sun bi matakan da gwamnati da hukumomin da abin ya shafa suka dauka, sun zauna a gida amma ba su dakatar da motsa jiki ba, domin a ganinsu, motsa jiki ya fi muhimmanci wajen kiyaye lafiyar jiki, da karfin jiki don tinkarar cututtuka da dama. (Zainab Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China